*HADIN NI'IMA DOMIN JINDADI HAƊIN KWAKWA DOMIN SAMUN WADA TACCIYAR NI'IMA GA MATAN AURE:*
*Hanyar Da Zakibi Kiyi Hadin Kwakwa*
*Shi hadin kwakwa yana da matukar amfani ga mata.*
Hadin kwakwa hadine wanda yake saukar ma mace da ni'imanta, a koda yaushe zataji ta cikin sha'awa da bukata kuma yana sa namiji yaji baya gajiya da biyan bukatarsa ta aure.
*Abubuwan da zaki nema sune kamar haka;*
◻ Kwakwa 🥥
◻ Madara peak 🥛
◻ Dabino 🫘
◻ kaninfari🥓
◻ Danyar citta🫚
*Bayani;* Zaki fasa kwakwan ki tsiyaye ruwan a cikin wani abu ki rufe, sai ki bare bawon kwakwan sai ki sami magogi sai ki goge kwakwan, idan kin goge saikiyi amfani da ruwan kaninfari sai ki markada kwakwanki da danyar citta kadan.
Bayan kin markada sai ki zuba ruwa ki tace ki cire dusar dama kuma a can gefe kin jika dabinonki sai ki markada dabinon, ki juye cikin wannan tattaciyar kwakwanki, ki zuba madara peak ki dauko wadannan ruwan kwakwar da kika fasa sai ki zuba a cikin wannan ruwan sai ki motsa, idan ya hade sai ki saka a
cikin firiji yayi sanyi ko kuma ki saka kankara, ki wuni kina sha. In sha Allah zaki ga abun mamaki. Hajiyata abun ba,a magana ga dandano ga saukar ni'ima 💃
0 Comments