Ticker

6/recent/ticker-posts

Header Ads Widget

Responsive Advertisement

TSARABAN YADDA AKE HADIN SPICES KALA-KALA A CIKIN GIDA


 TSARABAN SUNAYEN SPICES KALA-KALA DA KUMA YADDA AKE SARRAFASU TA HANYOYI DABAN-DABAN



SINADARAN GIRKI

A wannan post din nawa zaki samu takaitaccen bayani da idea yadda zakiyi anfani da sinadaran girki wato kayanwa kamshi na gida dana waje.


Wani jan hankali da zanyi anan shine,baa zabga spices a abinci,kadan kadan zaki dinga sakawa a girki,kuma kisan spices din da suke going well a kowanne girki,su kansu spices din sai kin san wanne ne yake tafiya da wanne,idan ba haka ba a karshe zaa rasa inda kamshin girkinki ya dosa!


1)CLOVES(Kanunfari):-kanunfari sinadari ne mai matukar dadi a girki,musammam idan kika gano yadda zakiyi anfani dashi,kuma da irin abincin da ya dace ki saka shi..

*Duk lokacin da Zaki tafasa nama ki jepa Dan kanunfari Guda 2 ko uku 

*idan zakiyi farfesun nama,kayan ciki,kifi ko kaza,ki tabbata kanunfari yana ciki.

*kanunfari yana dadi sosai a wajen anfani da nama,kuma a farkon girki ake saka shi!


2)BLACK PEPPER(masoro):-masoro yana da dadin kamshi idan kika iya anfani dashi,yadda zakiyi amfani dashi kuwa shine.


*duk lokacin da zakiyi fried rice dinki,ki daka shi tare da tafarnuwa,zakiji banbanci

*ki daka masoro da albasa idan zakiyi miyar yauki,taji daddawa da gyadar miya,zaki ji banbanci!


3) GARLIC(tafarnuwa) :-

Tafarnuwa sinadarin girki ce mai karawa abinci kamshi mai kwantar da hankalin mai chi,akwai hanyoyi da yawa yadda zakiyi anfani da ita..


*hada tafarnuwa da ginger ki saka a soup ko farfesun kayan ciki

*ki hada tafarnuwa da kanunfari ki saka a ruwan miyarki

*idan zakiyi (marinade) ki tabbata kin saka hadin tafarnuwa,ginger da kanunfari,kin hada su wuri daya kin daka su liqwi,ki saka a kaza ko nama..yana matukar dadi a wajen gashi,na nama ko kifi

*zaki iya daka ta ita kadai ki saka a jollof dinki

*amma kada ki soma anfani da ita a miyar yauki,dan kuwa baya dadi.

 

4) GINGER(citta):- basai nace komai ba game da citta ba saboda duk inda zaayi anfani da kanunfari,masoro toh tabbas citta tana da matsuguni a wurin, ita citta tana da banbancin kamshi da fresh ginger,fresh ginger yafi dadi a lokacin da zakiyi anfani da tafarnuwa,ita kuma citta alokacin da zakiyi anfani da ragowae yen uwanta su masoro da kanunfari.


5) KIMBA:-kimba itama tana cikin kayan kamshin da yawa mutane basu waye daita ba,tana matukar dadi idan zaki hada garin kununki na gero,ki tabbata tana ciki,ko kuma idan markaden kunune na hasara,shima a jefa ta ciki a markado da ita tare da sauran kayan kamshi su citta,kanunfari da masoro


6)NUTMEG(gyadarmiya) :

Idan ma bakya anfani da nutmeg to ki fara,saboda sinadari ce matukar kamshi a miyar yauki,kuka,kubewa karkashi da sauransu,tafi dadi ida kika hada ta da daddawa da masoro da yer citta kadan kika dakasu liqwi,ki saka a ruwan namanki idan zakiyi miyar yauki,kuma a farkon girki ake anfani ita,saboda idan ta dahu sosai,shine kamshinta zaifito sosai.


7) CINNAMON (girfa):- Ina son girki da cinnamon,akwai na gari akwai kuma na stick,yana matukar dadi a shyi mai kyan kanshi,kuma yana dadi a home made drinks kamar su tamarind drink,milk shakes,ana saka cinnamon a baked foods kamar chocolates cakes,swissrolls,cinnamon rolls ,ana garnishing dashi,ana matukar dadi a soup na kayan ciki da kuma soup din nama.


8) CURRY:- Curry sinadarin girki ne da kowa ya sanshi amma ba lallai yadda yakamat kike anfani dashi ba, hanya mafi kyau yadda zakiyi anfani da curry shine ki sakashi a farkon girkinki da kuma tsakiyar girki,misala idan jollof rice zakiyi ana saka shi a farko wajen bayan kin tsaida ruwan jollof dinki,idanya tafasa,kika zuba shinkafarki,tayi tafasa kamar biyu sai ki qara..

 

9) THYME:- thyme yawanci anfi anfani da na kanti,amma akwai ganyen sa,wanda shima zaki iya anfani dashi ki saka a nama,kifi ko kaza, ana anfani da ganyen thyme a recipes na dankali yana matukar kawata abinci.


10) POTASH(kanwa):-

Akwai ungurnu,akwai jar kanwa akwai ,bakar kanwa da sauransu,amma anfi anfani da ungurnu da kuma bakar kanwa,duk dai wacce kike anfani da ita,ba lokacin da zakiyi anfani da ita yakamata ki fara kokawar jikata ba,zaki samu robar lemo mai kyau ki wanke kanwarki ki zuba a robar sannan ki zuba ruwa ki cika tap,duk sanda zakiyi anfani da ita daman tana kusa sai tsiyaya a murfin robar ko chokali ki zuba a girkinki.


11) TUMERIC:- wannan indian spices ne ,zaki ganshi yallow shar,kanshinshi bashi da karfi,yana da kyau a girki,domin yana kawata girki da wannan kalar tasa,misali zaki iya saka a farar shinkafa,ki dafa dashi kiyi garnishing da carrots da kume peas,yana kayu sosai,ana saka shi a recipes na dankali,idan zaayi fried chips zakiga yayi kala mai kyau,abin shaawa.


12) PAPRIkA:- yana da dadi sosai a girki, gashi zaki ganshi da jar kala,ana saka shi stew,ana zaka shi a gashi kamar idan zakiyi gashin nama,kifi,kaza da sauransu,zakiga namanki yayi wani jar kala mai kyau,ana saka chi kuma a blend spice,idan zaki hada home made spices dinki


14) CHILL POWDER:- chill combination ne na wasu spice,irinsu chili ,cumin ,oregano,cayyene da sauransu, zaki ji chill powder yana kamshi na musamman,kuma ana anfani da shi a miya da kuma kashin nama


15) ALL SPICES:- all spice sinadarin girki ne mai zaman kansa,wanda da yawa mutane suna zaton wasu combination ne na spice,haka yake round kamae masoro ko kanunfari,yana da dadin kamshi a girki,ana saka shi a dahuwar nama,soup da kuma brown rice,ana saka shi a salad dressing da kuma spice mix.


16) OREGANO:- sinadrin girki ne,zakiji shi da lemony flavor yana going perfectly da garlic da kuma curry a girki.


17) BASIL:-wannan ganye ne wanda yake matukar dadi da kyau a pasta recipes ,kuma ana saka shi a sandwich da burger da sauransu.


18) CILLANTRO/ CORIANDER:- da yawa anacewa cilantro da coriander leaves daya ne,kwai babncin suna ne aka samu, zaki ganshi kamar parsely leaves,sai dai yafi parsely haske,ana saka shi a recipe na nama,kaza,kifi da kuma vegetables.


19) PARSELY:- parsely ganye ne kore shar,mai kyau a girki da kuma dadin kamshi,ana saka shi a minced meat,ko baked food,ana garnishing dashi,kuma ana saka shi a pasta recipe da recipes na dankali,yana kawata girki sosai.


20) CHIVES:- chieves shine lawashin albasa,yana da dadi a nama,ko fate,ko kuma recipes na dambu,yana da kyau a wajen garnish,ana saka shi a recipes na dankali,zaki iya barinshi ya bushe,idan zakiyi wani recipe na flour ki marmasa shi,zai baki kala mai kyau,ko ki marnasashi a bread crumbs shima yana kyau,ko a saka shi a kwai idan zaka soya.


21) MINT LEAVES:- Shine ganyen na'ana'a, dayawa an shayi ake anfani dashi,ana anfani da shi a recipes na drinks,kamar lemon tsamiya,mango drinks,milk shakes da sauransu,kuma yana dadi sosai a girki,ganshinsa yana da karfi,kadan ake saka wa a girki.


22) SPINACH:- Spinach shine allayyahu ana saka shi a miyar agushi,miyar ganye,miyar taushes da sauransu,ana sakashi a alala,fate da kuma jollofs.ana saka shi ne a karshen girki.


23) CUMIN:-sinarin girki zaki ganshi kanar buntun shinkafa, ana saka shi a kayn kamshi spices,kamar idan zakiyi home made spice,spice blend, ana saka shi a stews.


24)CARDAMOM:-cardamon spices ne na indian cuisine,yana da dadin kamshi a girki,ana saka shi tare da su kanunfari ko cinnamon,kuna ana saka shi a baked foods.


25) MEAT TENDARIZER:- sinadarin girki ne da ake sakawa a nama,especially nama mai tauri,zaki fara sakawa a nama yayi wasu yen mintuna sannan ki dora,yana taimakawa sosai namanki ya dahu da wuri.


26) SPICES:-wannan combination ne na kayn kamshi,yan matukse dadi a brown rice ,fried spagetti da kuma soups.



Post a Comment

0 Comments