YANDA AKE SARRAFA A SOYA NAMAN LAYYA A LOKACIN BABBAR SALLAH YAYI DADI SOSAI
Dayake lokacin babbar sallah anfi yanka shanu,raguna,da kuma Dan taure,Sai kuma tantan🥩 da ake Yi tare da yanka kaji🍗. Haka kuma soyawa ce kadai hanyarda aka Fi bi domin ajiye Naman sallah, saboda hakan zamu kawo maku hanyoyi da dama da ake sarrafa Jan Nama,naman kaji,kayan ciki,tare da ganda/Kai/kafafu In shaa Allah...
YADDA AKE SOYA NAMAN LAYYA YAYI DADI
Da farko zaki yanka Naman in to pieces Sai ki wanke kitsaneshi ki zuba atukunya kisa gishiri, Maggi star curry or farin maggi tare da albasa ki zuba a tukunya sai garlic idan da BUKATA ki rife ba tare da kin saka ruwa a ciki ba,zai soma silala (zakigan ruwa sun taru acikjnsa) ki barshi kan wuta har Sai ruwan ya kone,ya soma soya kansa Sai ki zuba man gyada ko kitse/kakide idan kina da shi ki soya Naman, da hakan har ki kammala sai ki kawo yankakken koren tattasan ki dakika dan soyashi da albasa da tarugu Dan daidai ammafa saikinada bukatar su idan bakiso shikenan sai garin yaji naki da kika daka domin Naman sallah ki zuba akai tin da zafinsa ki juya su hade jikinsu,shikenan kin kammala...
Idan kuma irin mutanen yankin sokoto ne da suke gashi kafin a soya shi ma yankawa kawai zaki Yi ki zuba a tukunya tare da gishiri,maggi albasa su tsane jikinsu Sai ki zuba mai a soya...
______✍️By Chef Oum Aslam & meenat kitchen 👩🍳
0 Comments