Ticker

6/recent/ticker-posts

Header Ads Widget

Responsive Advertisement

YADDA AKEYIN HADADDEN DAMBUN NAMA MAI KAMAR AUDUGA


YADDA AKEYIN DANBUN NAMA WANDA ZAIYI MAI KAMAR AUDUGA


✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤

(INGREDIENTS)

✤ Tsokar Nama

✤ tarugu 

✤ albasa 

✤ tattasai

✤ kayan Kamshi

✤ curry

✤ maggi dasauran spices

✤ mangyada

✤ tafarnuwa idan dabukata


           METHODS

Uwargida zaki wanke namanki kisashi acikin kwando ruwan ya tsane idan ya tsanene saiki dauko tukunyanki ki zuba shi saiki yanka albasa kisa kayan qamshi da Maggi dasauran spices dinki yaji albasa saiki daura a wuta idan kinsaka saiki rufe ki dauko tarugu albasa tattasai ki gyara kisa aturmi ki daka kokiyi grating idan yadaku zaki iya barin saikinxo dakawa kisa maggi aciki da kayan qamshi idan naman ya dahu saiki tsame ba,asaka ruwa atafashen sbd INGREDIENTS din yakama jikinshi saiki dunga sakawa acikin turmin kina dakawa wato cikin wannan kayan miyan idan kin gama dakawa daman kin zuba mangyada acikin tukunyan suya to saiki saka wannan dakakkan naman naki acikin mai kifara suya.


ki tabbatar maggi ya shenye naman.daman kinsamo abin tatan kokanki kin wankeshi tsaf ya bushe saikita juya wannan naman dake cikin mai idan ya soyu zaki ga yafara zama kalan soyuwa.kada kuma kibari ya wuce hannu yadaiyi jan suya dinnan.saiki dauko abin tatan ki dunga kwashewa kina zuba acikin shi.

idan kin gama kisa hannu kidunga matsewa harsai kin tabbatar man ya fita.wai uwargida aradu akwai zafi.sbd gaskiya saikin daure zakisha zafi sosai.amma matse man dakyau.shi zaisa yasama audugan dan haka idan kin daure shikenan to uwargida shikenan kinyi danbunki mai auduga.

 

✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤


       *(HANYA TA BIYU)* 


idan uwargida ta tafasa namanta.da komai da komai yanda nasa a na farkoncan.to sai jajjaga kayan miyanki ki zuba aciki ki tabari wannan ruwan naman ya qone acikin naman..sai ruwan yakusan tsotsewa sakisamu mucciyan tuqa tuwanki kiyita tuqawa kaman yanda kike tuqa tuwo.koda naman irin na rago me uban qashi dinan ne.to uwargida karkidamu da saikin ware qashin daban kafin.a a.kina iyayi kina tuqawa naman nafita cikin qashin to kina cire qashinto nan mazakiga yanata zama auduga to uwargida a nanma zaki gyayazama kaman auduga.

 

✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤✤


     *(HANYA TA UKU)* 


uwargida zaki iya samun namanki tsoka bayan kin wankeshi tas kin tafasa to wannan hanyan inkinada injinyin niqa wato blender naman to dashi zakiyi aiki idan kinyi niqashi sai kisaka man kadan a tukunya kifara soyashi daman yariga yazama audugan tun farkon daki ka niqashi a wannan blander so saiki soya shi batare da kin cika maiba to uwargida na barki anan.


kar incikaki da zance idan Allah ya nufa anyi layya to in bai bai nufaba to sai adau hakuri uwargida kada adauka da zafi aita kwantarwa maigida hankali da da dadan kalamai batare da annuna gajiyawaba.

sbd halin da muke ciki a yanzun sai mundunga kwantarwa mazajan namu hankali muna tausasa kalamai masu dadi, to uwargida saina zo cin rangam kardai amanta da Chef Oum Aslam🥰 a aikomin danawa naman sallahn ta yanar gizo🤣😍.


 ~____✍🏻✍🏻 Chef Oum Aslam & meenat kitchen👩🏻‍🍳~



Post a Comment

0 Comments