Ticker

6/recent/ticker-posts

Header Ads Widget

Responsive Advertisement

YADDA AKEYIN HADADDEN DAMBUN NAMAN KAZA MAI DADI


 YADDA AKEYIN HADADDEN DAMBUN NAMAN KAJI


INGREDIENTS

Kaji

Tattasai,

tarugu,

albasa da tafarnuwa,

oil

Kanunfari,

masoro,

citta,

thyme,

curry,

kimba,

nutmeg,

cinnamon,

knorr and onga cube,

salt.


     PROCEDURE:


A wanke kaza da kyau a zuba a tukunya, sai a zuba ruwa yanda kazar zata dahu luguf kuma ruwan ya tsotse a jikinta. Sai ki zuba dakakkan spices dana ambata, tare da knorr dasu gishiri. Sai a barta tayi ta nuna. Bayan ya nuna sai ki sauke, ki samu abun da zaki tuqa dashi, sai ki yi ta farfasa kazan kina tuqe shi tare da cire qasusuwan, idan kina tuqewa zaki ga ya koma babu wani naman da bai fashe ya koma kamar niqaqqen nama ba. In kuma baki son wahala wasu a turmi mai kyau suke juyewa, wasu kuma a blender kowa dai akwai nashi. Saboda so ake ya tuqu ya zama babu salen naman. Idan kin gama sai ki ďandana maggi da sauran spices idan basu fito ba yanda kike so sai ki ďan qara. Amma kaďan saboda idan naman ya soyu maggin zai fito dayawa.


Sai ki jajjaga kayan miyanki ďan dai-dai tare da tafarnuwa ki zuba a kai a juya ya hade. Sai ki ďaura non stick pot a wuta ki zuba mai ďan dai-dai a bari yayi zafi amma ba sosai ba, sai a ďebo kajin a zuba a cigaba da juyawa har sai yayi golden brown. Zaki iya yi kina qara mai amma a kula saboda kada yayi yawa ana ci ana tatse mai.


Daga nan sai ki juye a tray, idan akwai ragowar sai ki sake zuba mai sannan ki sake zubawa. In an gama duka sai ki zauna ki sake rage duk wani abun da baki so da ragowar qananun qasusuwa na ba a rasa ba.


Note: Dambu in kina son ragewa kanki wahala kada kice har tuqawar akan wuta zaki yi. Saboda ga zafin wuta gashi kina juyawa duk sai ki qone. Sannan koda baki da tukunyar da bata kamawa (non stick) to ki yi qoqarin canza tukunya sai ki fara soyawa dashi, yanda mai zai kasance a farko kafin a zuba naman. Sannan kowa zaki ji yana cewa dambun nama mai kamar audiga ban san wani abu da ake sawa dambu yayi haka ba. Kawai ya danganta da irin tuke naman da kika yi kafin ki fara soya shi. Don haka yawan tuqawanki yanayin yanda dambun zai kasance. Ina son dambun kaza, ke na wanne kika fi so?😋🤗

 *_____✍🏻✍🏻By Chef Oum Aslam & meenat kitchen👩🏻‍🍳*



Post a Comment

0 Comments