YADDA AKEYIN SPECIAL HADADDEN ALKAKI MAI DADIN GASKE
INGREDIENTS:-
1. Alkama kwano daya
2. Sugar gwangwani 6
3. Nono na shanu
4. Man shanu danye
5. Butter simas rabi
6. Mai kwalba biyu
YADDA AKE HADAWA
Uwargida ta sheqe alkama ta cire dukkan dattin, ko ta wanke ta baza shi a rana ya bushe. Sai ta kai babban inji a mishi barjin fate idan aka dawo dashi a bude tsakiyar alkaman a kwanon kwabi a juye nonon shanu, butter, man shanu, sai a murje shi da kyau ya hade sosai. Sannan sai a zuba ruwa amma kwabi za tayi mishi mai qarfin gaske yanda zai hade da kyar, sai ta rufe shi ta bari ya kwana.
Idan ta tashi da safe sai t jiqa kanwa, ta rinqa yayyafa masa tana hada shi tana bugawa. Har sai ta diba a hannun ta masa nadin alkakin ta ga bai karye ba. Wato ta yi tsaho dashi ta murza duka bai karye ba. Kenan ba qaramin bugu zata masa ba. Kuma ba a jibga masa ruwa sam, yayyafa masa za ta rinqa yi tana buga shi.
Sai ta zuba sugar a tukunya, ta zuba ruwa kamar kofi uku ta dora a wuta. Idan mai buqatar sugar alkakin ya rinqa diga ne bayan ya gama shiga cikin sa sai ta saka tsamiya kwaya daya ko (table spoon na lemun tsami) yayin da take dafawa. In kuma tana son ya bushe a jikin sa kamar wanda zan turo to kada ta sa.
Wurin dafa sugar ta kula yana fara yin kumfar farko na dahuwa ta diba a cokali yana dan fara shan iska zata ga yayi danqo. Sai ta sauke don haka kada ta barshi yayi ta dahuwa kamar na tuwon madara ko aya.
Sannan wurin soya alkakin ta saka mai aqalla kwalba biyu ko fiye, baya shan mai sam amma yana buqatar mai wurin soya shi. Kuma wutan kadan-kadan yanda cikin zai soyu. Bayan ta tsane shi a mai kai tsaye a cikin sugar zata saka, idan tana gabda tsamewa sai ta kwashe na cikin sugar din ta sa a kwanon da zata ajiye.
NOTE: Idan ta yi wanda bata so sugar yana bin sa ne zai dan rinqa daskarewa sai tana yi tana dan narkar dashi.
Sannan ludayin da zata rinqa amfani dashi wurin suya daban, na sakawa a sugar shima daban. Wa'yanda basu iya nadin shi ba su nemi wa'yanda suka iya su koya musu. Sannan zaku ga wasu alkakin su yayi ja wasu sun yi haske yanayin alkaman ne amma babu damuwa.
*_____✍🏻✍🏻By Chef Oum Aslam & meenat kitchen 👩🏻🍳*
0 Comments