YADDA AKEYIN KAYATACCEN DAMBUN SHINKAFA MAI DADI
Duk da kasancewar shinkafa tuni ta zama abinci na yau da kullum kuma gama garin abincin da kowane gida sai ka ganta, amma idan uwargida ta san kanta da kyau za ta iya sarrafa shinkafa ta yadda za ta fitar da dahuwa da za ta ja ra’ayin iyalin gida wajen cin abinda ta girka.
Yana da matukar kyau a ce uwargida tana da nau’o’in abinci kala daban-daban ta yadda ba zata gundiri maigida da yaranta da nau’in abinci daya zuwa biyu ba.
A saboda haka DAMBUN SHINKAFA na daya daga cikin nau’in girke-girken da uwargida ya kamata ta kara a taskarta Na Sirrin girke-girke.
INGREDIENTS:-
– Shinkafa
– Karas
– Koren wake
– kabeji
– albasa
– attaruhu
– Sinadarin dandano
– gishiri
– hanta
– man gyada
YADDA AKE WANNAN HAƊIN DAMBUN
Da farko dai za ki samu shinkafarki iya adadin da ki ke bukata, ki kai a barzo miki. Ki fidda garin ta hanyar tankadewa ki dauki tsakin ki wanke shi tas! Ki zuba amadanbaci, ki rufe ruf da leda sannan ki daura a wuta ki kawo murfi ki rufe dan ba’aso tiririn ya dinga fita. Ki tabbatar kin zuba ruwa a kasan tukunyar daidai yadda ba zai kone ba.
Ki tafasa karas dinki sama-sama. Ba lugub ba ki yayyanka shi bayan kin kankare bayan. Shima koren wakenki tafasa shi, akwai wanda ake siyarwa bararre kuma busasshe to da shi za ki amfani.
Kabejin ma ki wanke shi tas ki yanka amma ba kanana can ba.
Attaruhu da albasa ki yankasu su ma yadda ki ke bukata. Ana so albasar ta yi yawa. Hantarki k itafasa da isasshen sinadarin dandano da dan gishiri, ki yanka gutsi-gutsi.
Bayan tsakinki ya yi laushi sai ki sauke ki zuba mai ya kama shi, sannan ki kawo kayan lambun nan ki zuba, ki cakuda su yadda za su hade jikinsu da tsakin haka ma attaruhu da albasar nan hade da yankakken hantarna nan ki hada ki sake juyawa, sannan kidan da ka sinadarin dandano da gishiri kadan yadda ba zai yi yawa ba ki cakuda, ki mayar wuta.
Ki bashi lokaci za ki ji yana fidda kamshi sosai, ki tabbatar ya yi kamshi kuma ya dahu sosai yadda ake so, saiki sauke shikenan sai ayi amfani da mangyada saici😋.
*______✍🏻✍🏻By Chef Oum Aslam & meenat kitchen👩🏻🍳*
0 Comments