Ticker

6/recent/ticker-posts

Header Ads Widget

Responsive Advertisement

YANDA AKE AJIYE NAMAN KAI KAFAFU TARE DA GANDA NA DAN WANI LOKACI DOMIN AMFANIN BAYAN SALLAH


 YANDA AKE AJIYE NAMAN KAI KAFAFU TARE DA GANDA NA DAN WANI LOKACI DOMIN AMFANIN BAYAN SALLAH 



Kasancewar lokacin sallah mutane da dama sun rage kwadayin Nama ,hakan ke sanya idan ma an dafa Naman Kai /kafa/ganda Sai ya kasance ba kowa ke ci ba,saboda akwai koshin sa... Hakan zai sanya idan aka ajiye shi zuwa bayan sallah aka dafa ,za ayi ribibinsa in shaa Allah.Hakan ya sanya zamu kawo maku yanda ake ajiye shi na wani dan lokaci.


Da farko bayan an gama yanka ragon layya,bayan an shigo da Kai da kafafun shanu/ragon/fata Sai ki gasa su sosai akan wuta/gawayi ki tabbatar ciki da wajen su sun gasu sosai ta yanda ko'ina na su ya qame jikinsa Sai a Kai a jiye gurinda zai rika shan iska ,In shaa Allah ba abinda zaiyi matuqar iska yana ratsa shi.... Dik lokacinda za a yi amfani da shi,sai a jika shi a ruwa a wanke tas Sai a dafa irin dahuwarda ake buqata.


Ko kuma bayan kin gasa shi a wuta/garwashi ciki da wajensa ya gasu sosai Sai a zuba a cikin baho da ruwa a wanke shi tas Sai a soya a ruwan man gyada a tsane a kwando idan ya bushe Sai a ajiye gurinda zai rika shan iska,In shaa ba zaiyi komai ba...


Ko kuma bayan kin gasa kin wanke tas Sai a saka a Leda a daure a ajiye a fridge Wanda yake sanyi baya yanke masa ko kuma yake da kankara. In shaa Allah ba zaiyi komai ba har izuwa lokacinda za a tashi amfani da shi...



Post a Comment

0 Comments