KUSKURE GUDA (50) ALOKACIN BAWA YARO TARBIYYA.
---1. Bawa yaro nono a kwance
---2. Sawa yaro suna mara kyau
---3. Barin yaro da kazanta.
---4. Rashin jan yaro a jika.
---5. Kin ciki idan ya shiga.
---6. Rashin nemawa yara iyaye nagari.
---7. Sabawa ka’idojin shari’a a wurin saduwa.
---8. Yawan bacin rai da tashin hankali ga uwa yayin da take da ciki.
---9. Rashin aikata ladduba da sharia ta shinfida da zarar an haifi yaro.
---10. Daukar yaro, ko bashi nono duk lokacin da yayi kuka.
---11. Rashin tsara lokacin shayarwa.
---12. Wuce ka’idar lokacin daya dace a shayar da yaro.
---13. Rashin sawa yaro tsoron Allah a zuci sai na iyaye.
---14. Fifita wani a tsakanin‘yaya.
---15. Daurewa yaro gindi in yayi laifi ko tsokana.
---16. Bawa yaro ko sayamasa duk abinda yanema.
---17. Rashin koyawa yaro shiga irin ta musulunci.
---18. Rashin kai zuciya nesa in yaro yayi laifi.
---19. Rashin koyawa yaro yanda zaiyi Magana da nagaba dashi.
---20. Rashin sanin gurin da yaro yake zuwa idan yafita.
---21. Rashin sa yaro a makarantar data dace.
---22. Rashin koyawa yaro yadda zai karbi bako.
---23. Sayawa yaro kayan wasan da basu daceba.
---24. Sawa yaro abinci yai taci ba iyaka.
---25. Koyawa yaro mummunar shiga ta hanyar shigar da iyaye sukeyi.
---26. Rashin karantar halin yaro dayi masa hukunci da daya daga cikin halayen ‘yan uwansa.
---27. Tilastawa yaro yayi abinda bazai iyaba.
---28. Zabawa yaro fannin dazai karanta alhali bashi yake soba, ko bazai iya yinsaba.
---29. Yawan zagi da iyaye sukeyi a gaban yaro.
---30. Hana yaro yin wasa alokacinsa.
---31. Sanya fina finai marasa kyau, Yaro yana gani.
---32. Yiwa ‘yaya auren dole.
---33. Rashin manufa daya tsakanin iyaye.
---34. Hora yaro ta hanyar hanashi abinci, ko barinsa da yinwa, bayan da akwai abincin da za’a bashi.
---35. Bawa yaro umarni da yabawa juna.
---36. Barin yara maza da mata suna cudanyar data sabawa shari’a.
---37. Barin yara suna zuwa bukukuwa barkatai.
---38. Dorawa yara maza ko mata talla.
---39. Rashin yiwa yara bayanin sabon yanayin da zasu fuskanta idan sun kusa balaga.
---40. Kin tsayarwa da yarinya manemi daya, da barinta tana harka da samari barkatai.
---41. Barin yarinya ace sai takawo miji dakanta sannan za’a yimata aure.
---42. Barin ‘ya mace ta dade tana karatu, kamar tagama jami’a batare da miji ko wani tsayaiyen manemiba.
---43. Nunawa yarinya ko yaro cewa aure yana hana karatu.
---44. Rashin kyakkwawar manufa gurin neman aure.
---45. Yawan dukan yaro,ko duka ba a bisa ka’idaba, ko daukar duka abisa sahun farko na hora yaro.
---46. Kyale yaro idan yanata zaro Magana barkatai.
---47. Yiwa uwa fada, ko cin zarafin miji a gaban‘yaya.
---48. Yiwa yaro fada agaban ‘yan uwansa.
---49. Rashin daukar matakin daya dace idan yaro yayi laifi.
---50. Rashin koyawa yaro tattali.
Wadannan sune abubuwa guda 50 da suke lalata tarbiyyar yaro.
Da fatan zamuyi aiki da
wannan nasiha Allah Yayi muku Albarka yan uwa,
0 Comments