*YANDA AKEYIN HAƊIN SABULUN DILKA*
*Sabulun gana*
*Sabulun salo*
*Jan gana*
*Sabulun carrot*
*Sabulun Madara*
*Sabulun cocomba*
*Man zaitun*
*Man kwakwa*
*Dilka*
*Lalle*
*Kurkur, amma me kyau wanda ba'a hadashi da komai ba na ainihin cittar* *kurkur*
*Majigi*
*Lemon tsami*
*YANDA ZAKI HADA* *:-*
Da farko zaka samu roba ka yayyanka sabulanka waje daya, ko ka goga su za'a hadesu ne duka guri daya sabulan sai a zuba dilka da yawa itada kurkur din in mutum yatashi zubawa zai duba kimar yawan sabulunsa ne sai a zuba sai lalle dan misali sai a jujjuya su sai s zuba man zaitun dana kwakwa a Dada juyawa sai a samu turmi a daka majigi sai a zuba akar a juya sai a rika zuba ruwan lemon tsami a hankali ana juyawa bayan an gama hadewa in mutum yanaso ya hade sosai sai ya zuba a turmi yasan kara dakawa dan ya hade sosai shikenan sabulun dilka ya hadu in har ya karbeka to fatarka zatayi kyau sosai,
~Chef Oum Aslam & meenat ✍️👩🍳~
0 Comments