AMAFANIN LEMON TSAMI GA MASU KARANCIN MANIYY,DA KUMA ILLAR SA GA LAFIYA.
Idan ka karanta ka turawa sauran yan uwa domin su amfana.
Alakar lemon tsami da maniyi Bincike ya nuna cewa akwai alaka mai karfi tsakanin lemon tsami da maniyin namiji, musamman ta bangaren samar da kwan halitta, yana taimakawa wajen kara karfin gudun maniyi. Akwai sinadaran Vitamin C da thiamine a cikin lemon tsami, wanda ke bunkasa kwan haihuwa ta hanyar kara karfi ga maniyi. Dangane da ikirarin wasu na cewar lemon tsami na tsinka maniyi, Hajiya Jummai Hassan wacce kwararriyar likita ce kan abinci a asibitin Wuse a Abuja, ta karyata hakan.
Ta bayyana cewa ruwan lemun tsamin da ake matsawa a ruwa ko a shayi a sha bai kai yawan da zai tsinka maniyi ba, illa ma dai zai gyara da inganta shi. Sai dai wani bincike da aka gudanar a kasar Australia na nuni da cewa, shan lemon tsami mai yawa a lokaci daya na tsinka maniyi, hakan illa ne ga iyalan da ke son ba da tazarar haihuwa.
Yadda zaai amfani da lemon tsani ta hanyar daya dace.
Matakin farko na amfani da lemon tsami shine yin amfani da shi a lokacin da aka yanka shi. Za a iya amfani da shi a ruwa, salads, zuma ko a cikin shayi, wani lemon ko cinnamon. Ka samu ruwa kofi daya, ka matsa lemun tsami guda daya, idan kana so, ka hada da zuma. Irin wannan hadin ana so a shashi kafin ayi karin kumallo. Bincike ya nuna cewa cin yayan itatuwa masu dauke da sinadarin Vitamin C kamar lemon tsami, na rage hatsarin kamuwa da cutar zuciya ko shanyewar rabin jiki.
Masana kiwon lafiya sun tabbatar da cewa, duk da tarin amfanin lemon tsami ga lafiyar dan Adam, hakan bai hana lemon tsamin zama mai illa ba, musamman ga masu ciwon gyambon ciki. Kasancewar lemon tsami na dauke da sinadarin asid mai yawa, kuma gyambon ciki (ulcer) na gaba da asid,
Hakan na iya daga ciwon da zaran mai dauke da shi ya sha lemon tsami. Kwararriyar likitar abinci a asibitrin Wuse Hajiya Jummai, ta bayyana cewa, lemon tsami yana illa ne kawai ga masu dauke da cututtukan da ke adawa da asid a cikin su. Ga mutanen da jikinsu ke zabar nau'ikan abincin da suke so, da yawansu lemon tsami na sanya su yin amai ko zafin zuciya da kumburin jiki, a cewar mujallar Healthline.
0 Comments