Ticker

6/recent/ticker-posts

Header Ads Widget

Responsive Advertisement

KADAN DAGA CIKIN MATSALOLIN DA AKE SAMU WAJEN SHAYAR DA YARO NONO


 KADAN DAGA CIKIN MATSALOLIN DA AKE SAMU WAJEN SHAYAR DA YARO NONO!!



 *Sharing ma sadaka ce* 


Tabbas iyaye dayawa sunayin kurakurai da dama wajen shayar da yaro, ga kadan daga ciki :


1- Basa barin bakin Nonon yashiga bakin yaron gabaki daya. 

      Amfiso idan za ashayar da yaro nono , bakin nono wajen bakinnan duk yashiga bakin yaro, Sabida idan baishiga bakinsa sosai ba, yana shan iska, wannan iskan shi yake saka Yara kumburin ciki wani lokoci harda hararwa. 


2- Shayar da yaro a kwance : Ba daidai bane a shayar da yaro a kwance , sabida akoi hanyar da ta hada Makwagoro,  Kunne Da Hanci , To ta wannan hanyar ruwan nono yakan bi yaje kunne wanda hakan yana kawo ciwon kunne na yara.


3- Canzawa yaro nono : za kaga mata da dama idan sunsa yaro a daya Nonon tuni za kaga suncire sun maida zuwa daya Nonon. 

     Amfison idan ansa yaro a nono abarshi yai tashan daya Nonon har sai yakoshi, dalili kuwa bincike Ya nuna yaro idan yafara shan nono, Ruwan Nonon Farko da zaizo ruwa ne kadai, sai ruwan yagama zuwa abincin zaizo. Kinga kuwa idan Kinyi saurin maida shi zuwa daya Nonon kin chika cikinsa da ruwa babu abinci sai kiga yaro cikin dare yana kukan yinwa ke kina tunanin ciwon ciki ne kiyi ta dura masa magani a banza. 


4- Bawa Yara kanana ruwa kafin wata shida : Tabbas duk wani ruwa da za'abawa yaro kafin wata shidda zai iya cutar da yaro, kuma gurbaccecen ruwa ne, idan ruwan randa ne akoi cututtuka wanda ido baya gani idan babba yasha zai iya jurewa amma yaro bashida garkuwan jikin da zai karesu, idan ruwan Faro ne ma akoi chemicals a ciki,  yana daga cikin illar bada ruwa duk yaron da akabashi ruwa bazai barshi nono Ya isheshi ba. 


Kadan daga cikin amfanin shayar da yaro nono Zallah har zuwa wata shida :


1- Yana Kara musu basira 

2- Yana Kara musu garkuwan jiki 

3- Yana karesu daga cututtuka 

4- Yana Kara musu Ilmi. 

5- Yana Hana yaro mummunar Kiba da mummunar ramewa.

6- Yana Kara soyayya tsakanin uwa da da.



Post a Comment

0 Comments