Ticker

6/recent/ticker-posts

Header Ads Widget

Responsive Advertisement

SIRRIN DAHUWAR CICCIBI


SIRRIN YADDA AKEYIN DAHUWAR CICCIBI


🅰️cikin darusa da nake turawa cikin group akwai irin wannan domin a fahimta tareda tabbatarwa har faifan bidiyo nayi, yanda ake dafawa amma akwai ƙarin bayani daya kamata a ƙara sani akansa,


🅰️kwai mata masu matsalar buɗewa ta ciki wanda yana faruwane bayan mace ta haifu batayi gyaran jiki akan lokaci ba ko kuma bata samu shawara akan me zata yi ba, yayin da wajen ya koma ya warke zai buɗe koda ta waje yana haɗe, musamman idan ya zama babu ni'ima a wadace, sai yarinƙa fitar da isaka ko lokacin jima'i ne,


🅰️na iya cin wannan garin koda kuwa da naman saniya bawai sai lalle naman gabanta ba, amma idan kin tabbatar zaki samu gaban saniyar kuma ƙaramar saniya da bata taɓa haihuwa ba, idan kuma naman ne shima zaiyi sosai amma anaso naman cinya na saniya ƙarama sai asamu tsokar a yanka, sai a tsoma a nonon Raƙumi, sannan a yanka farar albasa, sai kuma a zuba garin ciccibin a kayi yanda zai manne ajikin naman, yanda akeyin tsire haka zakiyi, sannan ki saka a farar leda saiki daure sannan ki dafa acikin tukunya me ruwa zallah aciki,


Bayan kin tabbatar ya dafu yayi laushi saiki sauƙe ki bude kowanne leda da kika ƙule, wanda dama anso kiyi kamar leda uku yayi sama, shikenan ki cinye naman duka, basai an saka masa kowanne kayan miyaba 


 Amma idan gaban saniya ne anayin farfesu kawai da garin aciki, matsalar ki da wannan haɗin kawai ace baki iyaba ko kiyi kuskure wajen haɗa garin, amma idan dai kinyi komai daidai to keda kanki zakiji daidai, ballantana miji zaiji kamar ƙaramar yarinya, kina iya cinsa a kowanne mako kiyi sau ɗaya na tsawon mako uku, ya danganta damatsalar ki,


Sai bayanin yanda ake haɗa garin ana buƙatar kayan haɗi guda goma wanda duka na gargajiya ne ingantattu,


(1) 'ya'yan Ruma fada


(2) kananfari


(3) kirfat


(4) citta me gora


(5) ɗan kumasa


(6) 'ya'yan minanas


(7) saiwar rawaya


(8) 'ya'yan tafashiya


(9) sassaƙen gabaruwa


(10) 'ya'yan kargo


Waɗannan duka anaso adadinsu ya zama ɗaya, za'ayita dakawa sai sunyi laushi.






Post a Comment

0 Comments