Ticker

6/recent/ticker-posts

Header Ads Widget

Responsive Advertisement

YADDA ZAKI ZAUNA DA NAMIJI MAI SAURIN FUSHI


 YADDA ZAKI ZAUNA DA NAMIJI MAI SAURIN FUSHI:



shi fushi dabi'ahce ta dan adam kowanna mutum yana fushi akwai sanadaran fushi acikin kwakwalai da suke a tara wanda dan adam ke gadosu daga iyayen sa IDAN KANA DA SANADARAN DAYAWA SAI KAZAMA ME SAURIN FUSHI KENAN.


IDAN MACE TA AURI NAMIJI ME SAURIN FUSHI TO TANA CIKIN MATSALA IDAN BATABI A HANKALI BA WATARANA AKAN ABU KADAN ZAIMATA DUKA YA FARFASA MATA JIKI HARDA KARYA HAKORI WANI KAN IYA KARYAWA MACE QAFA MA .


yar uwa inkina da namiji me yawan fushi to ana so kizama me lura sosai da wadannan abubuwa


*■ meye yake saurin sa shi fushi da tunzura?


*■ meye yake saurin sauko dashi in yayi fushi ?


*■ Wani namijin bayasan yawan surutu in yana jin yunwa, ko in yadawo daga gun aiki.


*■ wani namijinn yakan ji saurin fushi in bashi da kudi ko yaje sana'arsa bai samo komaiba.

Wani kuma yafi fushi da bata rai in yasami kudi ko ya dauki albashi duk dan karki dameshi da kinmatsa kuwa za abata.


*■ wani idan aka batamasa rai a waje koda a musune sai ya dawo gida da fushi dazarar kin tsokanoshi kadan sai ki taka sawun barawa yai tai miki masifa inba kiya sa a bama yai miki duka.


*■ wani baya so yanai miki magana kema kinai masa magana sai yai fushi da harzuqa zaiga kinma raina shi yana magana kina magana yafisu in yafada kiyi shuru har sai yagama.


WANI KUMA HAKAN YATSANA

YAFISO YANA FADA KINA FADA DA KINYI SHURU SAI YADAUKA KIN RAINA SHINE.


wani kuma baya son gatse ko zolaya ko yawan wasa nandanan sai ya hau fushi.


Dan haka ke zaki karanci halin mijinki kisan yadda yake dakuma hanyoyin da zakina mu amalantarsa. 


*■ SANNAN DOLE KI ZAMA ME HAAKURI FIYE DA KOWACCE MACE AMMA INBA HAKABA GIDANKI ZAIZAMA FAGEN DAGA

SAIKIGA KUNFUTA DABAN A UNGUWA YAYAN KUMA HAKA ZASUTASO.


TAYAYA ZA A CANJA DABI'AR SAURIN FUSHI? 


** aiki da ilmi da tarbiyyar muslunci sune kadai zasu saita mutum me yawan fushi

domin akan sami me tarin ilmi amma baya aiki da ilmin saikaga da ransa yabacci ya tabka wani rasshin da'ar.


Amma duk me aiki da ilminsa da ransa yabaci yayi fushi to zai nemi taimakon Allah sai kuga yaqi yanke hukunci cikin fushi kamar yadda Manzon rahama s.a.w ya umarta.


Domin shi fushi dabi ace ajikin rai baka da ikon hana kanka jinsa AMMA SAAI ANNABIN RAHAMA YACEMA KAZAMA ME MALLAKAR ZUCIYARKA A YAYIN FUSHI.


YAKUMA HANAKA YANKE HUKUNCI A YAYIN FUSHI.


DAFATAN MAZAJE MASU SAURIN FUSHI DA MATANSU ZASU LURA SU RAGE sugane raunin dake tattare da su na hankali tunani hali da dakuma jiki.



Post a Comment

0 Comments