Ticker

6/recent/ticker-posts

Header Ads Widget

Responsive Advertisement

ALAMOMI 30 DA MUTUM ZAI GANE AKWAI ALJANI A JIKINSA KO KUMA AN YI MASA SIHIRI


 ALAMOMI 30 DA MUTUM ZAI GANE AKWAI ALJANI A JIKINSA KO KUMA AN YI MASA SIHIRI.


1.) Rashin son karatun Alkur'ani ko sauraron karatun. 


2.) Rashin son yin ibada kamar sallah ko kuma yinta a cikin bacin rai da kasala. 


3.) Yawan ciwon kai mai tsanani ko tsagin kai ko kuma jiri.


4.) Yawan ciwon mara ko baya ko kwankwaso ko kuma ciki wanda ba ya jin magani. 


5.) Yawan jin tafiyar wani abu a jiki kamar kiyashi ko tsutsa ko kwarkwata tana yawo a jikinka amma in ka duba ba za ka ga komai ba.


6.) Yawan mafarke mafarke na ban tsoro ko firgirta da surutai a cikin bacci ko kuma ka ji wani abu mai nauyi ya danne ka ko ya shake ma ka wuya.


7.) Yawan jin tsoro ko faduwar gaba ko wani abu ya ringa yi ma ka gizo ko kuma ka ji kamar ana kiran sunanka amma ba ka ga kowa ba. 


8.) Yawan jin sanyi ko zafi ko rikewar kafa ko wani sashe na jiki.


9.) Rashin iya bacci da daddare ko yawan jin motsin wani abu ko surutai ko kuma takun tafiya.


10.) Rashin son yin kitso ko kuma ki ji ba kya so  a taba miki kai.


11.) Yawan bacin rai ko jin haushin mutane ba tare da wani dalili ba. 


12.) Rashin son shiga cikin mutane ko yawan zargin su ko kuma yawa rigima da su. 


13.) Yawan kuka ko dariya ba tare da wani dalili ba.


14.) Yawan jin kamar ana yi ma ka rada a kunne ko a ringa raya ma ka  a zuciya akan ka aikata wani lefin kamar kisan kai ko zina ko kuma sata.


15.) Rashin son yin Aure kl gamuwa da matsaloli kanana amma sai maganar auren ta lalace.


16.) Daukewar Sha'awa ko rashin jin dadin saduwa da iyali ko kuma tsanar abokin zama da wulakanta shi ba tare da wani dalili ba. 


17.) Yawan kallon mudubi ko Sha'awar kallon tsiraici.


 18.) Yawan son kade-kade da raye-raye.


19.) Yawan son dare ko cikin duhun ko yin shuru kamar ba ka gurin.


20.) Rikicewar Jinin Al'da ko na Nifasi.


21.) Rashin Haihuwa ko yawan Bari ko Haihuwar dan babu rai ko kuma wasu matsaloli su biyo bayan Haihuwa kamar jijjiga. 


22.) Aikata wani abu ba a cikin hankalin ka ba, sai daga baya ka ringa nadama ko mamakin yadda akayi ka aikata. 


23.) Yankewar jiki a fadi kasa ba a cikin hayyaci ba ko kurma ehu da rugawa a guje ba tare da ka san inda zaki ba.


24.) Yawan wasiwasi ko mantuwa acikin dukkanin Al'amura musamman a lokacin ibada. 


25.) Tabuwar kwakwalwa ko kasa fahimtar ko wane irin abu.


 26.) Rashin tsafta da son zama cikin kazanta da da dauda. 


27.) Yawan fita waje mara dalili ko tarewa a wani wuri kamar karkashin bishiya, kan bola, bandaki, jeji, bakin ruwa, da sauran su.


 28.) Rashin lafiyar da za'a kasa gane kanta. 


29. Rashin son Wa'azi ko zama da mutanen kirki.


30.) Yawan jin tsoron Rukuya ko masu yinta. Allahu Ta'ala A'alam.



Post a Comment

0 Comments