WANI BABBAN SIRRI GUDA 2 AJIKIN TUMFAFIYA DA YAKE MAGANCE WADANNAN CUTUTTUKA GA MATA DA MAZA WANDA YAKAMATA KOWA YASANI
Sirri guda ɗaya mata da maza duka na iyayi amma sirri guda ɗayan mata zallah ne,
Bari mu fara da sirri na farko da maza da mata ke iya amfani da kwanson jikin ƴaƴanta da ganyenta wajen maganin karya sihiri ko maganin jinnu, menene kwansonta? kwanson tumfafiya ana nufin ƙwallon dake fita ajikinta wannan akeso guda ɗaya da ganyen shima guda ɗaya abari su bushe sama sama sai ayi garinsu shima kada yayi laushi sai a haɗa da garin habbatussauda sai arinƙa hayaƙin ɗaki kafin a kwanta barci, amma a ɗaki kaɗai ake hayaƙin,
yawan munanan mafarkai razana cikin barchi, tayarda iska, yawan ganene, yawan wasi wasi, abun nufi kayi abu amma karinƙa tantamar ko kayi, waɗannan duka sunada alaƙa da jinnu insha allahu idan aka riƙe wannan za'ayi Nasara,
To sai hanya ta biyu wanda mata kaɗai ke iya aiki da ita shine yin gumba da furenta, gumbar furen tumfafiya akwai kyau asalin kayan matane wanda ko ina ana iya shiga dashi sannan kowacce mace kika bawa taci zata yaba saita baki labari amma saidai akwai ɗan wahala kasancewar anaso kowanne abu asaka adadinsa yanda zaiyi ƙaramin kuskure zaisa tayi tsami ko tasaki gudawa, ammafa maganin ni ima ne sosai idan kinacinta abun daɗin koda kina al'ada zaki iya cinta,
Bari muyi misali da gero gwangwani ɗaya sai ayi garinsa ba sai an surfaba amma sai an soyashi, kananfari ana saka kwaya biyar sai kwakwa wanda za'a soyata itama bayan an gurazata anaso adadin kwakwar ya zama ɗaya bisa huɗu na wannan geron abun nufi kamar ki raba geron kashi huɗu to adadin kwakwar haka zai zama, duka ki haɗesu waje ɗaya ki saka furen TUMFAFIYAR ɗanyarta kamar adadin kwakwar ita mazarkwaila ana saka kaɗan amma ki tabbatar baki saka yanda zaƙinta zai fito sosai ba, daga nan saiki zubasu duka a tukunya ki saka ruwa kaɗan suna dafuwa sun zama gumba kina iya dakasu a turmi domin su haɗe shikenan kin gama.
0 Comments