Ticker

6/recent/ticker-posts

Header Ads Widget

Responsive Advertisement

DUK MACEN DATAYI DACEN AUREN NAMIJI MAI IRIN WADANNAN HALAYEN TAYI DACE A RAYUWA


 DUK MACEN DATAYI DACEN AUREN NAMIJI MAI IRIN WADANNAN HALAYEN TAYI DACE A RAYUWA


Mata kalilan ne suke dacen zaman aure. Hakan kuwa yana faruwa ne saboda sakaci wasu matan suke yi na zaban mijin aure. 


Wani lokacin kuma mazan ne suke canzawa bayan auren.


_Sai dai ga duk matar datayi dacen auren namiji mai wadannan halayen zai yi wahalar gaske ko ta sake iya zama da wani namijin bayan rabuwa ko mutuwa.


Wadannan halayen kuwa 

sun hada da:

 

1: Nuna Mata Soyayya Na Zahiri Da Badini: Duk namijin data yi dacen namiji da yake nuna mata soyayya a gabanta da bayan ta, wannan matar tayi dacen zaman aure.


2: Kula Da Bukatunki: Idan har kinyi dacen auren namiji wanda ya damu da damuwarki, tabbas kinyi dacen samun miji. 

Ba duk maza bane suke damuwa da abunda ya damu matansa. Amma da zaran mace ta samu mijin da yake kula da damuwanta, tayi dacen aure.


3: Baki Lokaci: Kamin aure Zaki ga yadda maza suke damuwa su baki lokaci. Duk lokacinda kike son ganinsa nan take zai zo. Amma bayan aure gaki gashi sai  kuma kiga bai baki lokaci.

Wasu mazan sun fi baiwa aiyukansu ko sana'ar su mahimmanci fiye da matansu. Irin Wadannan maza basu ware lokacinda zasu zauna da matansu domin yin hira ko tattaunawa masu ma'ana. 


Kamin auren namiji ya rika kaiki yawon cin kwalama, ko ya sayo ya kawo miki gida. Amma kuna aure sai kiga ko unguwa baya son fita dake bare kuma ya kaiki yawon cin kwalama.

Wannan yasa duk matar datayi dacen mijinta yana da lokacinta. Tabbas wannan matar tayi dacen aure.


4: Idan Yana Miki Kyankyawan Fahimta: Akwai mazan da suke da wuyar sha'ani. Mazane da ba a iya musu. Duk abunda mace zata musu sai sunyi mita ko fada.

Muddin kika samu mijin da yake da fahimta, tabbas kinyi dacen aure. 


5: Mai Baki Hakuri Idan Ya Batamiki; Ba duk maza bane suke ajiye girmansu su baiwa mace hakuri a lokacin da suka bata mata rai. Hakan yasa ba karamin dace bane wajen macen data sa'ar auren namijin da yake amsa kuskurensa kuma ya baki hakuri.

 

6: Namiji Mai Kawaici: Wasu mazan basu da hakuri ko kadan. Da zaran anyi musu abu bisa kuskure basu da kawaicin da zasu kauda kai su tari gaba. 

Dace ne mace ta samu mijinta mai kauda kansa ga kananan kurakurai zata morewa zaman aurenta.


7: Yarda Da Aminci: Musamman a wannan lokacin da mata da maza, manya da kanana suke amfani da shafuka daban daban na sadarwan zamani. Kishi da rashin yarda ya yawaita tsakanin ma'aurata.


Muddin har mace ta auri namijin da yake nuna mata yarda 100 bisa 100, ko shakka babu wannan matar bazata samu matsala a gidan aurenta ba.


8: Mai Kaunar 'Yan Uwanki: Wasu mazan babu ruwansu da 'yan uwan matarsa. Bai nuna musu kulawa ko kauna a duk lokacinda suka ziyarci matarsa ko kuma suka hade a wani mu'amala.

Idan har Allah Ya albarkaceki da samun namijin da yake nunawa na kusa dake kauna da soyaya. Tabbas kinyi dacen aure.


9:  Mai Karfafa Miki: Wasu mazan tamkar suna bakin ciki da samun matansu. Hakan yasa mace komai burinta na rayuwa sai irin wadannan maza sun dakile da sunan suke da iko akan mace.

Kina samun namiji da zai goya miki baya da karfafa miki gwaiwa na cimma burinki na rayuwa tabbas kin dace da aure.


10: Namiji Mai Kula Da Addininki: Akwai mazan da basu damu da kula da addini ba, bare ma asaran cewa zai koyawa matarsa addini.

Irin wadannan mazan abunda ke gabansu shine kawai lamari basu da lokacin yin addini bare koyawa wani idan ma mai illimin kika aura.

Dace da auren namiji mai kula da addini fa'ida ne a rayuwar macen data auri irinsa.

 

Wadannan wasu ne daga cikin halayen maza da duk wata mace zata yi fata da burin aure a rayuwarta.

Da fatan mata zasu natsu wajen kula ga irin mazan da suka zo neman aurensu domin zabo na gari.



Post a Comment

0 Comments