Ticker

6/recent/ticker-posts

Header Ads Widget

Responsive Advertisement

YADDA AKEYIN HADADDEN PANCAKE DIN AYABA


 YADDA AKEYIN HADADDEN PANCAKE DIN AYABA

 


ABUBUWAN DA AKE BUKATA



1- Ayaba

2- Fulawa

3- Suga

4- Baking soda

5- Gishiri

6- Dunkulen dandano

7- Kwai

8- Man gyada

9- Vanilla flavour (Optional)

10- Madara ta ruwa



YADDA AKE HADAWA


Uwargida ta samu kwano ta zuba fulawa kamar gwangwani biyu ko iya adadin da take bukata sai ta dauko baking soda ta zuba cikin babban cokali daya, sannan ta dauko suga ta zuba cikin babban cokali biyu, sai ta zuba gishiri cikin karamin cokali daya, sannan marmasa dunkulen dandano daya, sai ta cakuda hadin ta ajiye kada ta kwaba a haka zata barshi kawai.


Sannan sai ta dora karamar tukunya da ruwa a wuta bayan yayi zafi sai ta dauko ayaba kamar biyu ko uku ko adadin da takeso sai ta saka a ruwa ta dafa ayabar sama-sama bayan tayi laushi sai ta sauke idan zafin ya ragu sai ta bare fatar ayaban ta dama ta a ludayi sosai, sannan ta dauko wannan hadin tuwan kwan sai ta rika debo wannan damammiyar ayabar tana zubawa a cikin kwan tana dama su tare har sai ta kare sai tasa ludayi babba ko tayi amfani da 'Mixer' ta hannu tayi ta damasu sosai.


Daga nan sai ta dauko wani kwanon ta fasa kwai guda biyu sai ta karkada shi sosai sannan ta dauko madara ta ruwa kamar gwangwani daya sai ta juye a ciki, sai ta dauko man gyada ta zuba cikin babban cokali daya sai ta sake karkadawa sosai sannan ta ajiye.


Daga nan sai ta dauko wannan hadin fulawar data ajiye sai ta rika debowa tana zubawa a kwabin ayaba da kwan nan tana zubawa tana juyawa a hankali har kwabin ya daidaita bawai sai fulawar ta kare duka ba, anaso dai kwabin yayi ruwa-ruwa kadan kamar kwabin kwainar fulawa ('Yar langwai) to sai ta ajiye, sannan ta dauko flavour na vanilla sai ta zuba cikin murfin sa ko cikin karamin cokali 1 sai ta gauraya sosai , sannan sai ta dauko kaskon suya ta dora a wuta bayan ya danyi zabi sai ta dan zuba mai kadan sannan ta debo wannan hadin tana zubawa akai tana soyawa kamar dai (Wainar fulawa) din haka zata rika soyawa daban daban har ta kammala.



Post a Comment

0 Comments