Ticker

6/recent/ticker-posts

Header Ads Widget

Responsive Advertisement

KALAMAN SOYAYYA MASU SANYA MASOYA MURMUSHI CIKIN KAUNAR JUNANSU


 KALAMAN SOYAYYA MASU SANYA MASOYA MURMUSHI🥰❤️


 

 TA ‘DAYA. Ina son dukkan taurarin da suke bisan sama, amma ba za’a hada son da na ke yi musu da kuma na wadda ta ke a cikin idanuwan ki ba, ina son ki.


TA BIYU. Lokaci yana nan zuwa da zaki mallakawa wani zuciyar ki, ina mai yin kira a gare ki da ki tabbatar da cewa kin mallakawa wanda ba zai raunata zuciyar ki ta hanyar yaudara ko cin amana ba, saboda ita zuciya d’ayace babu wadda zaki dauko ki sauya a lokacin da bakin ciki da damuwa suka mamaye zuciyar ta ki.


TA UKU. Yanzu haka ina cikin farin ciki, shin kin kuwa san mene ne dalili? Hmm saboda na kasance mai sa’a, kin kuwa san tayaya? Saboda Allah ya na so na, kin kuwa san me ya sanya na ce haka? Saboda ya ba ni wata babbar kyauta, kin kuwa san mene ne? Ba komai ba ne ba face KE masoyiyata, ina son ki.


TA HU’DU. A koda yaushe lokaci tashi yake yi tamkar tsuntsu, amma ita soyayyar mu kullum ginuwa ta ke tare da kara samun wajen zama a cikin zuciyoyin mu karda ki manta da ni ki kasance mai yin tinani na kamar yadda nima na kasance a ko da yaushe.


TA BIYAR. Abun da na ke ji a dangane da ke gaskiya ne kema na san kin san da haka cewa ina son ki, a duk lokacin da kika bar ni ba zan iya motsawa ko da nan da can ba, wannan shi ne abun da zai faru da ni a duk lokacin da na rasa ki.


TA SHIDA. SO tamkar wata sarkar zinari ce da ta d’aure zuciyoyin mu a waje guda, a dukkan lokacin da kika tsinka waccan sarka tofa ki tabbatar da cewa tamkar kin kore farin ciki ne daga cikin zuciya ta.


TA BAKWAI. Salim ina son ka, me ya sanya ka ke yin kokwanto a bisa kalmar so da na furta a gare ka? Tabbas kaine mutum na farko da haduwa da shi ya kore min bakin ciki, ya wanzar da farin ciki a zuciya ta ya yalwata murmushi a saman fuska ta hakane dalilin da ya sanya na ke kiran ka da SADAUKI.


 Salim, ka yi nasara ka yi nasarar jan ra’ayin soyayya ta a kan ka kaine na mallakawa linzamin zuciyata, kaine mutum na farko da na taba furtawa kalmar SO kuma a yanzuma zan kara mai-maitawa a gare ka ina son ka.


Ka amince mu yi tsaftatacciyar soyayya. Sai yanzu na gano cewa a duniya babu abun da ya kai samun masoyi dad’i, a duk lokacin da na rasaka ban san halin da zan shigaba, daga karshe ina mai sanar da kai cewa buri na yanzu bai wuce na ganin ranar da zaka zamo ango ni kuma na zamo mata a gare ka ba, ina alfahari da kai a duk inda na kasance, ka huta lafiya daga mai son ganin farin cikin ka a koda yaushe.



Post a Comment

0 Comments