HANYOYIN DA ZAKU SARRAFA KWAI KALA-KALA GA UWARGIDA DA AMARYA
CIKAYI SANTI
INGREDIENTS:
* Kwai
* Nama
* Curry
* Maggi
* Gishiri
* Tumatir
PROCEDURES:
Ki dafa kwanki, daidai yawan da kike so ki yanka shi kanana, ki yanka tumatir, attarugu da albasa akai ki yanka tafasasshen namanki kanana a kai, ki fasa kwan ki zuba akai, kisa maggi, curry, gishiri, ki kada ya kadu sosai, ki dora mai a kan wuta ki soya kamar suyar wainar kwai.
SUYAR KWAI MAI NAMA
INGREDIENTS:
* kwai
* Nama
* Maggi da gishiri
* Curry
* Albasa
* Attarugu
PROCEDURES:
Ki tafasa namanki da maggi, curry, thyme, albasa, ki daka shi sosai, ki fasa kwai ki yanka albasa, attarugu, ki zuba dakakken nama, ki karo maggi da gishiri daidai yadda kike so, ki kada sosai, ki soya kamar wainar kwai.
NAMA CIKIN KWAI
INGREDIENTS:
* Kwai
* Nama
* Gishiri da Maggi
* Albasa
* Attarugu
* Mai
PROCEDURES:
Ki dafa kwanki daidai yawan da kikeso, kowanne ki yanke kasansa wajen fadin kadan ki kwakule kwanduwar a hankali ki cire ta, ki tafasa namanki da curry, thyme, maggi, gishiri. Idan ya dahu ki zuba attarugu kadan ki daka naman, sannan ki dinga debo dakakken naman kina turawa cikin kwai, idan ya cika sai ki debo kwanduwar ki toshe bakin kwan da ita, haka zakiyi tayi har ki gama, sannan ki dinga tsoma kwan a cikin ruwan kwai kina soyawa, idan ya soyu sai ki kwashe, wannan nama cikin kwan yana da dadi.
WAINAR KWAI MAI ALAYYAHU
INGREDIENTS:
* Kwai
* Hanta
* Alayyahu
* Curry
* Maggi da gishiri
* Albasa da Attarugu
* Manja ko Mai
PROCEDURES:
Ki yanka alayyahunki kanana, hantar ki daka ta, bayan kin dafe ki fasa kwai ki zuba hantar, ki zuba alayyahunki, curry, maggi, gishiri, da albasa, idan kina so, ki soyata kamar suyar wainar kwai.
WAINAR KWAN VEGETABLES DA KODA
Ingredients:
* Koda
* Kwai
* kabeji
* Peas
* Green peas
* Carrot
* Maggi da gishiri
* Curry
* Albasa da attarugu
PROCEDURES:
Ki yanka vegetables naki ki soya su sama-sama, ki fasa kwanki ki zuba maggi, curry, gishiri, ki tafasa kodarki ki yanka ta kanana, ki zuba akan kwan, ki zuba vegetables ki soya.
DAFAFFEN KWAI MAI DADI
INGREDIENTS:
* Kwai
* Albasa da Attarugu
* Curry
* Maggi da gishiri
PROCEDURES:
Ki fasa kwanki ta samansa amma fasawar yar karama zakiyi, ki zaggaga kwan a kwano, ki yanka attarugu da albasa ki zuba a kan kwan, ki zuba curry, gishiri da maggi daidai yadda dandanon zai yi miki, ki zuba mai kadan ki kada kwan sosai, sannan ki duddura kwan a cikin kwansonsa da kika juye, ki kawo solitef ki nannade kwan dashi sosai sai ki zuba ruwa a tukunya, ki jajjera kwan ki rufe ya dahu sannan ki sauke, zaki bare kamar yadda ake bare dafaffen kwai, bayan kin warware solief din. Akwai dadi sosai.
KOSAN KWAI
INGREDIENTS:
* Kwai
* Busasshen burodi
* Attarugu
* Maggi da gishiri
* Curry
* Albasa
* Mai
PROCEDURES:
Ki daka busasshen burodi, ki fasa kwai, ki yanka albasa, attarugu, maggi, gishiri, curry, ki zuba busasshen burodi ki juya yayi kwauri kamar kwabin kosai, ki dinga dibar kullin kina sawa a mai kina soyawa kamar kosai, idan yayi ja ki dinga kwashewa kina tsanewa da kwadanda.
ALALAN KWAI / AWARAR KWAI
INGREDIENTS:
* Kwai
* Kifin gwangwani
* Albasa da attarugu
* Maggi da gishiri
* Man gyada ko butter
PROCEDURES:
Ki bude Kifin gwangwaninki, ki dagargaza shi ya murmushe sosai, ki fasa kwan daidai yadda kike son yawan alalan, ki yanka albasa, attarugu, carrot, ki hada da peas ki zuba akan kwan, kisa gishiri, maggi, curry, ki zuba kifin akan kwan, ki buga sosai, ki zuba mai kadan ki shafa butter ko mai a gwangwani ki zuzzuba, ko ki kukkulla a leda, za ki iya ci haka idan ya dahu ko ki yayyanka kisa a ruwan kwai ki soya ta zama awarar kwai.
WAINAR KWAN DANKALI
INGREDIENTS:
* Kwai
* Dankali
* Nama
* Albasa
* Curry
* Maggi da gishiri
* Mai
PROCEDURES:
Ki dafa dankalinki ki marmasa, ki tafasa nama, curry, maggi da gishiri ki daka, ki tafasa kwai ki zuba dakakken naman da dankalin akan kwan ki yanka albasa, kisa gishiri, maggi da curry ki kada su hadu sosai ki soya kamar suyar kwai, ko ki gasa a oven.
✍🏻✍🏻Chef Oum Aslam & Meenat👩🏻🍳
0 Comments