KI KOYAWA KANANAN YARANKI, MUSAMMMAN 'YA'YAN KI MATA WADANNAN ABUBUWAN.
=================================================
🙋🏻Ki gargadi 'yar ki kada ta kuskura ta zauna a cinyar wani, koda kanin babanta ne ko Almajirin gidansu.
.
🙋🏻Kada ki dinga canja kaya a gaban 'ya'yanki wadanda suka kai kamar shekara biyu. Ki dinga cewa su fita.
.
🙋🏻Kada ki yarda wani babban mutum ya dinga kiran 'yar ki da "Mata ta" ko "Amarya ta" dds.
.
🙋🏻Idan 'ya'yanki suna wasa da wasu yaran, ki dinga lura wane irin wasa suke yi. Saboda wasu yaran suna wasa da al'aurar junansu.
.
🙋🏻Kada ki matsawa 'yar ki zuwa wajen wanda ba ta so ta je wajensa. Kamar wani me siyar da kayayyaki ko makamancinsu.
.
🙋🏻Ki saka lura sosai idan kika ga dan ki ko 'yar ki sun shaqu da wani mutum a waje kuma suna son zuwa wajensa.
.
🙋🏻 Kada ki bari dan ki ko 'yarki su dinga yawo ba riga ko wando a cikin gida balle su fita waje.
.
🙋🏻Idan kin yiwa 'yar ki kwalliya, to ki gaya mata iya gidajen da za ta shiga. Kuma daga nan ta dawo gida. Kada ta zauna a rariya ko shige-shigen gidaje.
.
🙋🏻 Idan ki ka ji an yiwa abokin dan ki ko kawar 'yarki wani abu mara dadi, to kema ki binciki na ki sosai. Ki tuhume shi.
.
🙋🏻Idan 'ya'yanki mata sun fara girma, ki koya musu yadda ake kula da jini. Da yadda ake kula da budurci da hadarin kawar da shi. In ba haka ba zata fara koyar munanan dabi'u a wajen kawaye.
.
🙋🏻Ki kula da irin kayan wasan da yaranki suke amfani da su. Kamar yartsana me hoton tsiraici da makamantansu.
.
🙋🏻 Ki koyawa 'yar ki me shekara uku yadda ake wanke muhimman gurare a jiki, har da kirji kuma ki gaya mata kada ta bari kowa ya ta6a mata nan wajen da nan wajen.
.
🙋🏻Ki tabbatar duk wani hoto ko abin amfani wanda zai 6ata tarbiyyar yaro kin nisanta shi da inda yaranki za su gani.
.
🙋🏻Duk sanda 'yarki ko danki ya kawo miki karar wani babba ya cire masa kaza ko ya ta6a masa kaza, to kada ki dau mas'alar da wasa. A bi duk matakan da suka dace don tabbatar da abinda ya faru.
.
.
Ku tuna Tarbiyyah tana farawa ne daga gida kuma iyaye maza da mata suna da haqqi babba na kula da tarbiyyar yara.
.
Wannan su ne kadan daga shawarwarin da zan bayar, da fatan iyayen mu mata za ku kula. Allah ya karemu tare da iyalenmu.Amin
0 Comments