YADDA AKEYIN GYARAN GASHI DA RUWAN SHINKAFA GA MATA:
Shin ko kin san cewa wanke gashinki da ruwan da aka wanke shinkafa yana kara abubuwa da dama?
Ruwan da aka wanke shinkafa da shi yana da sinadarai masu yawa dake kara wa gashi tsayi, kyau da kuma laushi.
Za ki iya wanke gashinki da ruwan shinkafa sau daya a sati domin samun wannan sakamako.
Ga matakan da za ki bi domin wanke gashinki da ruwan shinkafa kamar haka:
- Ki samo shinkafar ki me kyau, kofi daya ko kuma duk yadda kike so ta zama.
- Sai ki zuba wa shinkafar ruwa ki bar ta ta jiku na tsawon minti 20 zuwa 30.
- Ki rika yawan juya shinkafar saboda kar ta dunkule.
Idan ruwan ya komawa launin ruwan madara to hakan na nuna cewa ya yi yadda ake so.
Daga nan sai ki tace ki raba ruwan da shinkafar.
Sai ki jika gashinki a cikin ruwan, in zai yiwu ki bar shi ya jiku na kamar minti 30 zuwa 40.
Bayan haka sai ki wanke gashinki da ruwan sanyi ki taje shi har sai kin tabbatar duk wani abun shinkafar ya fita daga kanki.
Daga nan sai ki daure gashinki. Zaki ga abin mamaki idan kina yawan yin hakan.
Wadannan su ne matakan da ake bi wajen wanke gashi da ruwan shinkafa.
0 Comments