YADDA MATA ZASU HADA MAGANIN RIKICEWAR AL'ADA DA KANKU INSHA'ALLAHU:
A yau insha'Allah za mu yi bayani ne akan yadda za ki hada maganin rikicewar al'ada da kanki Insha'Allahu.
Wasu lokutan akan samu masu irin wannan matsalar, kuma yana wahalar da su sosai. tundaga ciwon mara, jiri da kuma
murdawan cikin wasu kuwa har kamar za su suma suke idan wannan larura ya taso masu, da dai sauransu, babban matsalar kuma ita ce idan mace tana da irin wannan matsala
na rikicewar al'ada to babu damar ta samu juna biyu.
idan lokacin al'adar ya kusa sai ki yi kokari ki hada wannan magani, idan kuma sai bayan kin fara ne kika ga wannan bayanin to kina iya haɗawa ki yi amfani da shi.
Abubuwan da za ki nema basu da wahalar samu sannan basu
da tsada.
(1) Za ki samu garin habbatussauda mai kyau din (ana sayar
da shi a Islamic chemist na ko'ina)
(2) Sai ki nemi ingantaccen zuma madaidaici ki saya.
(Idan kina so ki gane zuma din bashi da hadi, sai ki tsoma kan ashana a cikin zuman, bayan kin ciro ashanan sai ki kyatta shi a jikin kwalinsa.
idan ya kama zuman mai kyau ne, idan kuma bai kama ba to jabu ne).
GA YADDA AKE HADA MAGANIN:
Za ki nemo ruwan zafi madaidaici a kofin shan shayi, kamar yadda ake saka Lipton.
sai ki debo garin habbatussauda cokali
daya 'teaspoon' ki zuwa a cikin ruwan zafin da kika riga kika tanada.
sannan sai ki zuba zuman madai-daici, sannan sai ki
sa cokali ki kada domin su hade da juna. idan ya dan huce sai ki shanye duka.
Haka za ki rika yi safiya da yamma, kamar kwana ukku a jere.
Insha'Allah wannan matsala zai rabu da ke kuma komai naki
zai dawo dai-dai.
Bayan maganin matsalar rikicewar al'adar kuma zai yi maku maganin abubuwa da yawan gaske na matsalolin jiki da inganta lafiya.
Allah ya sa mu dace...
0 Comments