Ticker

6/recent/ticker-posts

Header Ads Widget

Responsive Advertisement

YADDA MATA ZASUYI GYARAN JIKINSU A LOKACIN SANYI DON SAMUN WADA TACCIYAR NI'IMA DA DUMIN JIKINSU


*(HOME OF GYARAN AURE) YADDA MATA ZASUYI GYARAN JIKINSU A LOKACIN SANYI DON SAMUN WADA TACCIYAR NI'IMA DA DUMIN JIKINSU*



A kowanne yanayi kika samu kanki kada kiyi wasa da kula da jikinki musamman irin wannan yanayi na sanyi da ake ciki,

kisani bakida wani abu a wannan duniyar sama da rayuwar aurenki shi kuma rayuwar aure babu maganar me kuɗi da talaka, tsohuwa ko yarinya kawai kiyi iya yanda zaki iya, mace bata tsufa saidai ita da kanta ta mayarda kanta tsohuwa, mata da yawa lokacin da suke ƙara shekaru a daidai lokacin miji ke ƙara kusantarsu saboda yanda suke maintain kansu,


Idan aka shiga lokacin sanyi jikin mace nada matukar muhimmanci a wajen namiji, 

maza suna bukatar kwana da  mace a gado ɗaya fiyeda lokacin zafi sannan namiji yana samun karin sha'awa fiyeda lokacin zafi dukda cewa mace sha'awarta na raguwa da kashi talatin cikin ɗari a lokacin sanyi amma gyaran jiki yana iya janyo hankalin miji wajen mace hakan kuwa na ƙarawa mace karfin guiwa wajen jure jima'i komai tsananin sanyi,


*ƊUMIN JIKI*  abu na farko shine ɗumin jiki wanda wannan bakya bukatar dogon bayani akayi kasancewar ga bayanai ta ko ina barkatai akan wannan kamar shayi da goriba da kananfari da citta wannan kada kiyi wasa dashi sannan shan ruwan kananfari da ɗuminsa shima yana temakawa mace jikinta ya zama da ɗumi a koda yaushe,


*LAUSHIN JIKI* bayan kinyi wanka da ruwan ɗumi kowanne mayi da zaki shafa a yanzu ya zama yanada maiƙo da saka gumin jiki sannan irin mayukan gargajiya na zogake da man kwakwa da man kaɗanya waɗannan duka mayuka ne masu saka laushin jikin mace,

*DUMIN GABA* akwai tsuguno da muka koyar koda ba irinsa ba matuƙar tsugunon zaisa gabanki yayi ɗumi kuma bazaisaki ƙaiƙayi ba to kina iyayinsa, koda bakida damar sabulu na almusk to kina zuba ruwan khal tuffah a ruwan ɗumi ya zama ruwan tsarkinki, wannan yana saka kowanne magani kikasha na ni'ima kiga aikinsa,


*ƊUMIN HANNU DA ƘAFA* waɗannan kada kiyi wasa dasu koda yake akwai halitta wasu tafin hannu da tafin ƙafarsu da tauri amma kisani wannan yana ragewa mace karsashi wajen gamsar da miji da rashin zaman ni'ima ajikinta, idan har kina cikin masu kaushin ƙafa ko taurin hannu to kitabbatar kina amfani da mayukan laushin fata tareda saka safa a ƙafarki,


Post a Comment

0 Comments