Ticker

6/recent/ticker-posts

Header Ads Widget

Responsive Advertisement

SIFFOFIN DA AKESON DUK WATA MACE TA KASANCE DASU A WAJEN MIJINTA DASU

SIFFOFIN DA'AKESON DUK WATA MACE TA KASANCE DASU A WAJEN MIJINTA


1:) Be Lovely: Ki zama mace ce wacce ta iya soyayya tana kuma nunawa mijinta tsananin soyayya.

Ki cire tunanin da wasu mata suke da shi idan namiji bai nuna musu soyayya suma bazasu nuna masa ba.

Gaskiya ne, shi soyayya 50/50 ya kamata, amma nunawa namiji matukar so ko da shi bai nuna miki, yana masa tasiri musamman a lokacin da bai kusa dake, ko yana tare da wacce bata iya yin hakan ba.

2:) Be Joyful: A duk lokacin da mijinki yake tare dake ya rika jin baya son rabuwa dake saboda yadda kike nishadantar da shi da irin kalmominki da barkwancinki.

Kada ki zama dunkum, ke kullum sai dai a miki hira baki iya yiwa miji hira ba. Ke kullum baki da kalamai masu dadi sai abinci ya kare, babu gas, kudin makarantan yara, muna da buki mako mai zuwa.

Ki iya nishadantar da mijinki da kalmomi masu dadi masu sashi dariya.

3:) Romantic: Duk wani namiji yana son mace mai shagwaba. Macen da take kareraye jiki da murya idan tana tare da mijinta.

Mace mai son zama ko kwanciya a jikin miji. Mace mai son shiga wanka ko cin abinci da mijinta. Mace mai maida kanta wata 'yar karama idan tana tare da mijinta.
Mace bata yiwa namiji tasiri a rayuwar sa idan bata iya yin rayuwa irin na kenwa da mai ita ba. Idan kika dameshi ya koreki ki kuma sake dawowa. A zahiri zaki dauka cewa tamkar namiji baya son irin wadannan matsin ne, sai lokacin da baki kusa da shi abun yake masa tasiri, duk abunda kika saba masa ko yi dashi muddin bai samu wannan abun daga gareki ba zai ji tamkar rayuwar sa bai cika ba a wannan lokacin.

4:) Be Kind: Namiji yana son yaga irin yadda mace take shiga ko take nuna damuwarta a lokacin da yake cikin rashn Lafiya, ko wata jaraba na rashin dukiya ko rai. A wannan lokacin yake iya tabbatar da kuma sanin hakikanin irin macen da yake rayuwa da ita.

Idan kika zama mace ce mara kulawa da tausayawa a lokacinda mijinki baida lafiya kin rikito. Idan kika zama mara hakuri da halin yau, kin kwafsa, idan baki damuwa da wani rashi da yayi daga cikin dukiyarsa ko kuma wani rasa rai da yayi, kin tashi daga aiki.

5:) Sexy: Anan ne wasu masu iya magana suke cewa ki zama katuwar mijinki. Kina ku biyu da mijinki amma kin rufe jikinki daga sama har kasa. Baya ganin motsawar hips bare kai kawo breast. Baki masa wawan zama da zai rika hango ki. Baki saka masa kananan kaya ko kayan baccin da zai rika ganin ki kina burgeshi.

Bazaki kalli mijinki kice masa yau ina son kwanciya ba. Baki iya fitowa fili ki masa hira ko yabamasa irin kwanciyar da kukeyi. Hajiya kin zama kurma da kuma bakin ki.

Mata da dama basusan cewa ba, daga lokacin da kika yiwa mijinki wata kalma da batsa ko kika masa a rubuce daga wannan lokacin shi kuma yake soma kamuwa da sha'awar ki ba.

Mace idan za a shekara 1000 muddin mijinta ba shi ya nemeta babu ruwanta da shi. Kina cutar kanki ne. Ya barki da ciwon al'ada duk wata, ya barki da ciwon ciki dana mara duk kullum.


Post a Comment

0 Comments