Ticker

6/recent/ticker-posts

Header Ads Widget

Responsive Advertisement

YADDA AKEYIN HADADDIYAR LEMON KANKANA DA KARAS


 YADDA AKEYIN LEMON KARAS DA LEMON KANKANA



Abubuwan hadawa


Karas

Cittah

Sugar

Flavour

 


YANDA AKE HADAWA


Da farko zaki wanke karas dinki ya wanku sosai sai ki yanka kanana ki zuba a bilenda. Sai ki wanke cittah itama kiyanka kanana ki zuba a bilenda kisa ruwa ki markada da karas dinki, yayi laushi. Sannan sai ki tace kisa sugar da flavour. Ki juya sosai sai ki sa a firinji yayi sanyi.


Shi karas yanada kyau sosai wajen kara lafiyar ido


LEMON KANKANA DA LEMON TSAMI


 KAYAN HADI


• Kankana

• Lemon tsami/ Lemonade

• Sukari/sirof

• Flavour

 

YADDA AKE HADAWA


Uwargida za ki fara dafa sukarinki ya zama ruwa amma fa kada ki bar shi ya kone idan ya dahu shi ne abin da ake kira sirof sai ki ajiye a gefe guda. Shi wannan sirof din ya fi saukin amfani a kan ki yi amfani da sukari na ainihi.


Sai ki yanka kankanarki ki fitar da kwallayen sannan ki markade yadda za ta yi laushi sosai. Sa ki samu kofin da kike hada lemo ki zuba a ciki sannan ki kawo lemon ana sayar da shi a manyan shagunan kayan masarufi idan kuma ba ki da shi za ki iya yin amfani da lemon tsami.


Idan kika matse sai ki ki tace shi da kyau ki tabbatar babu komai a ciki sai ki juye a kan kankanar nan sai ki dauko sirof dinki ki zuba ki kuma kawo filebo mai kanshin kankana ki zuba, sai ki juya ki sa a firiji don yin sanyi.



Post a Comment

0 Comments