Ticker

6/recent/ticker-posts

Header Ads Widget

Responsive Advertisement

YADDA AKEYIN HADADDIYAR SHINKAFA MAI 4 COLOURS KALA HUDU


 YADDA AKEYIN HADADDIYAR SHINKAFA MAI 4 COLOURS KALA HUDU



KAYAN HADI


1- Shinkafa

2- Koren wake 

3- Karas

4- Koren tattasai 

5- Tattasai 

6- Butter

7- Dafaffiyar masara

8- Man gyada

9- Gishiri, Curry, Thyme

10- Dunkulen maggi

11- Food Colour 

12- Nama ko kaza


Note: Wannan jerin kayan hadin ba duka ne suka zama dole sai anyi amfani dasu ba, misali kamar Masara ko Nama ko Kaza da Butter dan haka ya danganta da halin maigidanki ko kuma ra'ayinki wajen girkin.


 YADDA AKE HADAWA

_Da farko Uwargida zata dora nama ko kaza a wuta ta silala bayan ta gama sai ta tsame naman ta bar ruwan silalen a tukunya sannan sai ta kara ruwan sanwa akan wannan ruwan silalen adadin yadda take bukata sannan sai ta dauko nauyin kala da ake zubawa a abinci irin kalar da takeso ko ja ko koriya ko shudi (Foods colour) sannan sai ta zuba a ruwan sanwar har ya canja kala, sannan sai ta dauko shinkafa ta zuba mata tafasasshen ruwan zafi ta wanke ta sosai da ruwan sannan sai ta jira bayan mintuna biyar sai ta dauko shinkafar ta tsame ta zuba a ruwan sanwar ta rufe ta jira sai ta dahu.


_Daga nan bayan shinkafar ta dahu ta shanye ruwan sanwar sai uwargida ta sauke ta ajiye a gefe, sannan sai ta dauko farantin suya ko kaskon da take suya dashi ta dora a wuta ta zuba mai amma bada yawa ba sannan ta dauko butter kaman cikin babban cokali sai ta zuba ta hadasu da man har su nake.


_Daga nan sai ta dauko albasa ta yayyanka kanana ta zuba a cikin man, sai ta dauko koren tattasai da jan tattasai ta yayyanka kanana sosai sai ta zuba, sannan sai ta sake dauko koren wake da yankakken karas kanana suma ta zuba, sai ta sake dauko dafaffiyar masara itama ta zuba sai ta cakudasu ta jujjuya tana soyawa.


_Daga nan sai uwargida ta dauko Curry da thyme ta barbada sai ta sake dauko maggi da gishiri ta barbada (amma uwargida ta kula kada kayan dandanon suyi yawa), bayan ta zuba su duka sai ta dauko shinkafar ta zuba akan wannan hadin kaskon ta cakudasu tana soyawa (Idan shikafar tana da yawa kum


Daga nan sai uwargida ta dauko Curry da thyme ta barbada sai ta sake dauko maggi da gishiri ta barbada (amma uwargida ta kula kada kayan dandanon suyi yawa), bayan ta zuba su duka sai ta dauko shinkafar ta zuba akan wannan hadin kaskon ta cakudasu tana soyawa (Idan shikafar tana da yawa kuma ba zata soyu a kasko daya ba to sai ta raba wannan kayan hadin na kaskon gida biyu ko uku adadin yadda zata raba shinkafar sai ajiye ta dinga zubawa tana soyawa har ta kammala.


_Bayan ta kammala sai ta sauke ta dauko wannan naman ko kazar ta soyasu sai ta zuba akan abincin ko kuma kafin ta kammala abincin sai ta soya naman saboda ta gama atare basai ta jira abincin yadsa zai huce ba.


*Za a iya yin wannan abincin a ranar sallah ko lokacin biki ko suna ko wani party ko dinner na musamman.




Post a Comment

0 Comments