Ticker

6/recent/ticker-posts

Header Ads Widget

Responsive Advertisement

YADDA AKEYIN HADADDUN KALOLIN MIYAR ZAMANI GUDA GOMA SHA BIYAR 15


 YADDA AKEYIN HADADDUN KALOLIN MIYA GUDA GOMA SHA BIYAR 15 NA ZAMANI

 


Miyar efforiro

miyar zogale

miyar gyada

miyar wake

miyar albasa

miyar ugwu

miyar ridi

miyar ewedu

miyar ogbonno

miyar edikayinkong

miyar editan

miyar oha

miyar soyayyen agushi me albasa

miyar karkashi, kuka, kubewa

miyar shuwaka

 

MIYAR EFFORIRO


INGREDIENTS

kayan miya

nama ko kaza

crayfish

stockfish

kayan ciki

manja

alaiyhu

seasoning

spices

garlic

 

PROCEDURES

Ki sami stockfish k wanke k dafa k aje gefe. Naman d kayan cikin ma k tafasa d onions garlic seasoning d spices. sai k yayyanka tattasan, albasa, tumatir a tsaitsaye. K dora manja a wuta k xuba kayan miyar k soya k xuba crayfish dakakke da naman da kika dafa d stock fish dn kisa maggi salt spices ki rufe sai komai y dahu k sauke. Dama tuni kn wanke alaiyhun kn dafa ba tare da kn yanka ba sai k hada d miyar ki juya. Xaki iya ci da sakwara, tuwo DSS


 MIYAR SHUWAKA


 INGREDIENTS

shuwaka

hanta/koda

naman kaza/beef

dry fish

thyme curry

garlic, onions

kayan miya

manja

maggi,salt

egusi /makani

 

PROCEDURES

K wanke shuwaka don rage dacinta ta hanyar mitsike ta kina tace ruwan har sai kn dandana kn ji dacinta y ragu. Ki tafasa naman d hanta d koda d albasa,thyme, garlic d maggi, idan sun dahu sai k xuba markadadden kyn miya d soyayyen manja a kan tafasashen namanki idan yy kamar 7mns sai k zuba shuwaka, gyararren busashen kifinki d yankakkiyar albasa ki dandana abn d baiji ba ki kara sai ki barta ta karasa dahuwa. Xa a iya cinta haka ko kuma kina iya zuba egusi k markadadden makani. Aci dadi lpy.


MIYAR ZOGALE


INGREDIENTS

nama k chicken

busashen kifi

zogale

gyada

garlic thyme

seasoning spices

manja/na gyada

procedure

K tafasa namanki d thyme maggi garlic onion. Idan y tafasa ki zuba mai a wuta k soya k xuba kyn miyarki akan man ,ki xuba rwn naman akan kayan miyar, idan y soyu k kara ruwa kadan kmr ludayi 1 k zuba dakakkiyar gyada d gyararren busashen kifi d maggi d salt d curry, idan yy kamar 10mns sai k zuba zogalenki d kika gyara kika murje d hannunki, amma k zuba zogalen d yawa saboda da kauri ake son miyar. Ki sauke bayan kamar minti 15.


MIYAR GYADA


INGREDIENTS

nama

tantakwashi

kayan miya

gyada

kabewa

alaiyhu

daddawa

kayan kamshi

mai

seasoning spices

 

PROCEDURES

K tafasa naman d tantakwashi da onions garlic maggi, k xuba markadadden kayan miya a cikin man da kk soya, idan yy kamar minti goma yana soyuwa sai k xuba ruwan tafasar naman d tantakwashin, ki feraye kabewa k dafa k markada k zuba akan dafaffen kayan miyar k kara ruwa kamar ludayi 2 /3. K zuba dakakkiyar gyada ,sai kisa kayan kamshi da daddawa d maggi idan tayi kamar minti 25 sai ki zuba alaiyhun kamar minti 7 sai k sauke.


MIYAR WAKE

 

 INGREDIENTS

nama

wake

busashen kifi

kayan miya

mai

maggi salt

kayan kamshi

 

PROCEDURES

Ki tafasa namanki da onions, garlic maggi. Ki soya mai k xuba kayan miya a ciki, k zuba namanki da rwn naman k barshi y dahu kamar minti 15, sai k zuba gyararren busashen kifi , maggi, salt, d kayan kamshi d daddawa kadan idan kina so. Sai k zuba wakenki d kk surfa kika cire dusar kk dafa luguf, idan kn zuba wannan waken akan miyar sai k rufe y kara dahuwa Xa k ga waken y narke.


MIYAR SOYAYYEN AGUSHI ME ALBASA


INGREDIENTS

kayan ciki

nama

busashen kifi

kayan miya

agushi

manja/ na gyada

garlic thyme

seasoning spices

ugwu/ spinach

 

PROCEDURES

K tafasa k/ ciki d nama d gishiri,albasa, thyme, garlic .k soya manki idan y soyu sai ki xuba k/ miyar ki soya. K daka ko markada agushi d albasa sai k dora frying pan akan wuta k zuba mai k soya wannan agushi d kika markada d albasa.      

 Saimun hadu acigaban sauran kalolin miyarmu kukasance Dani Insha'Allahu.


 ✍🏻✍🏻Chef Oum Aslam & Meenat👩🏻‍🍳



Post a Comment

0 Comments