ABUBUWAN DA YAKE HAIFAR DA MATSALA TA ZUBAR JINI GA MATA MASU CIKI WANDA YAKAMATA KOWACCE MACE TAKIYAYESU
Ba kowane lokaci iyalai ke samun natsuwa ba matukar suka hadu ko suka fara ganin alamu na jini alhali suna da Ciki.
Akwai fitar jinin Da Bana matsala bane Wanda yake fita a Hankali Tare da Wasu ruwa wato sport haka wannan Yana daga cikin alamomin Implantation bleeding Wanda Nace
GANIN JINI KADAN KADAN LOKACIN DA MACE KEDA CIKI KASA DA WATA 2 BA MATSALA BACE SAI IDAN AN JAWOTA TA ZAMA MATSALA DAGA BAYA.
Mata Kashi 20% na Mata Kan hadu da wannan alamar da ake Kira (Implantation Bleeding) Wanda kwata kwata baya da matsala, baya daga cikin abunda ke zubar da ciki ko alama ta lalacewar ciki. Da dama Muna samun Mata da wannan yanayin musamman ga matan da Basu zarce Wata biyu da samun cikin ba.
Tada hankali da Matan kanyi musamman masu zumudin ciki ko wadanda suke da bukatan cikin Ido rufe ke JANYO wannan alamar ta zama matsala har ayi sanadiyar lalacewar cikin ta hanyar Anfani da wasu ababen da Kuma dena wasu ababen a gida, idan ma akai rashin Sa'a a asibiti ko chemist za a lalata cikin ko a zubar da shi Babu gaira Babu dalili wannan shine GARIN Nemo Kiba sai a samo Rama Allah ya Kyauta.
👉👉👉 Wannan jinin da ake gani Yana faruwa sanadiyar kyankyashashshen Kwan halittar Mace Daya Riga ya faru tsakanin sa da Sperm cells din Namiji Wanda daga karshe yayi Implantation din kansha cikin Mahaifar lokacin da yake wannan da Iznin Allah sai wannan jinin kadan kadan gami da majina majina su rika fita mace tarika ganinsu zuwa wani lokaci.
KU DAINA SHAN MAGUNGUNAN INFECTION DA SAURAN MAGUNGUNAN DA ZASU LALATA MAKU CIKI SANADIYAR WANNAN ALAMAR DA AKA GANI.
Ga hanyoyin da zakuyi Anfani dasu a gida Dan magance wannan ALAMAR cikin sauki.
1- Samun wadataccen Hutu.
2- Anfani da Pads Maimakon Tampons a gida ta yanda za a samu dadewar hanyoyin da jinin Kan biyo.
3- Anfani da Mild Pain relief kamar paracetamol ba irinsu Piroxicam ko Ibucap ba, matukar za ayi Anfani da kowane maganin rage radadi zai iya lalata Ciki.
4- Sannan zuwa asibiti mafi kusa da zaran anga abunda ba a ganeba, da Kuma kebentuwa da Anfani da Manyan magunguna na antibiotics da sunan mace nada infection.
5- Kebencewa Uwar gida, Ya zama wajibi Oga ya nade Mayafinsa har aga abunda Allah yayi na tsayawar jinin, Yin Juma'i wannan lokacin Yana daga cikin abunda ke zubar da cikin cikin sauki.
MANYAN ABUBUWA KO MATSALOLIN DAKE HAIFAR DA WANNAN YANAYI WATO ZUBAR JINI GA MACE MAI CIKI BA LOKACI KO BAYAN HAIHUWA BA.
Wadannan sune manyan ababen Dake Haifar da Wannan matsalar wacce take bukatar daukan Mataki ko kuma a rasa cikin.
1- MATSALA ta Cervix musamman Cervical Insufficiency.
2- Infection Ga Cervix
3- Placenta Previa
4- Preterm Labor
5- Uterine Repture
6- Plecenta Abruption
Za a iya fahimtar Matsala ce musamman ga matan da SUKA taba haihuwa Amma ga wadanda Basu taba haihuwa ba, ba Lallai bane a iya samun dukkan wadancen dalilan Dana zayyana.
Matakin farko da ake anfani dashi Shine a samu cikakken bayani ga mace, sannan Aune aunen Dake da àlaka da mahaifa, Cervix da sauran su..
0 Comments