Ticker

6/recent/ticker-posts

Header Ads Widget

Responsive Advertisement

YADDA AKE (HIGHLIGHTING) WATO BAYYANA WURAREN DA AKESO A KWALLIYA


 YADDA AKE (HIGHLIGHTING) WATO BAYYANA WURAREN DA AKESO A KWALLIYA


 

(bayyana wuraren da akeson bayyanawa a kwalliya)


Highlighting(bayyanawa, bayyana wuraren da akafiso agani, bayyana wuraren da akeso suyi haske akwalliya).


Shidai highlighting kamar yadda muka fada asama shine bayyana duk wani haske da akeson bayyanawa afuska ma ana(sune guraren da akefara gani akwalliya daga nesa)


wadannan wurare kuwa sunhadada:-


tsakiyar goshi ( tsaka tsakin jagira).

kan karan hanci

qasan idanu

qasan hanci ( saman baki).

haba ( qasan baki)

gefe dagefen baki xuwa qasan kunne.


Highlighter Dai kashi biyuce akwai cream ( meruwa) akwai kuma busashshiya.


cream highlighter shine meruwa dakike shafawa awuraren dayakamata kibayyana akwalliyarki, kuma ana shafa cream highlighter dazarar kingama shafa foundation kafin kishafa setting powder dinki. Anaso ashafa cream highlighter BBS ( Beauty blender sponge) saboda shiketaimakawa wajen blending komai tare yayi sumul.


cake highlighter( busashshyr highlighter) itakuma saikingama komai kinshafa setting powder a ilahirin fuskarki tukunna, sannan kidakko busashshiyar highlighter dinki kishafa awajn dakikai highlighting da brush.


Abubuwan da ake iyayin highlighting dasu naruwa(cream) sunhada da:


foundation wadda tafi wadda kikashafa a ilahirin fuskarki.

concealer (normal concealer dakike amfanida ita wajen shaping din girarki)

highlighter: sunanta kenan tanaxuwa amaxubi kala kala. Akwai me xuwa amaxubi kamr na qwanqwalati me murfi, akwai mekama da pencil etc.


Yadda zakiyi highlighting din shine:-


Zaki shashshafa cream highkighter a indakikeso kiyi highlighting kamr yadda mukai bayanin wuraren abaya, inkingama shafawa saikiyi blending (dandabewa)yabi fatarki sosai. Wannan shine yadda ake shafa cream highlighter. Kubiyini domin jin yadda ake contouring dakuma setting din fuska gabadaya.


 *✍🏻By Chef Oum Aslam Meenat💄👩🏻‍🍳*



Post a Comment

0 Comments