YADDA AKEYIN HADADDIYAR HADIN HALLAKA KWABO MAI DADIN GASKE
(Peanut Cake)
Uwargida barka da warhaka a yau ma kamar kullum muna tafe da wani salon girki wanda yasha ban ban da wanda muka saba kawowa a baya domin wannan baya cikin irin jerin abincin da akeyi domin aci a koshi sai dai ayi shi ne domin marmari, sannan wannan hanya ce da uwargida zata iya amfani da ita domin yin sana'a matukar ta bawa sana'ar muhimmanci to zata samu alkairi a jikin ta.
Kamar yadda kuka sani dai shi wannan girki ana yinsa ne da gyada to akwai hanyoyi biyu da ake bi wajen sarrafawa wanda zamu kawo muku su gaba daya a yanzu.
ABUBUWAN DA AKE BUKATA
1- Gyada
2- Sugar
3- Butter (Optional)
YADDA AKE HADAWA
Uwargida ta karamar tukunya ko karamin kaskon suya sai ta dora a wuta sannan ta dauko butter sai ta zuba kamar cikin babban cokali daya bayan ta narke sai ta dauko sugar kamar gwangwani daya ko biyu (adadin yawan gyadar da zata hada din, misali idan gyadar gwangwani biyu ce to sai tasa sugar din gwangwani daya ya isa), sai ta zuba a cikin butter din ta barshi ya narke sosai to kada ta sauke da wuri.
To daga nan sai ta dauko gyadar anfi son wacce aka soya marar bawo amma ko b a soya bama ba matsala to sai ta juye a kwano mai karfi ko ta zuba a karamin turmi sai ta dan daddaka sama-sama sannan ta kwashe ta ajiye.
Daga nan ta koma kan wannan sugar da butter din dake kan wuta sai taci gaba da juyawa yana dahuwa har sai ya canja kala sosai ya zama kalar *Coffee* to sai ta dan saka cokali ta debo kadan sai ta zuba a faranti bayan minti daya zata ga bushe yayi tauri sosai to alamar hadin ya dahu kenan to sai ta dauko wannan gyadar ta juye a cikin sugan dake kan wuta sai ta cakuda sosai bayan mintuna biyu ko uku sai ta sauke amma tana sauke sai ta juye a faranti mai fadi babba.
Bayan ta juye a farantin ya dan sha iska sai ta dauko wuka ta yayyanka gida gida dai dai girman da take bukata sannan sai ta banbare daga farantin kada ya kame ajiki ta rarraba su a hankali.
HANYA TA BIYU
A wannan bangaren ba a amfani da butter kawau uwargida za ta dora tukunya a wuta ne sai ta dauko sugar ta zuba ta barshi ya narke sai ta dauko gyadar ta daka ta sosai tayi laushi ba kamar a hadin farko da zata daka sama sama ba a wannan karon gyadar sai tayi laushi sosai sannan sai ta sauke wannan sugar data dafa sai dauko wannan garin gyadar ta zuba a ciki sai ta rika tukawa kamar tukin tuwo sai ta ya hadu sosai amma kada gyadar tayiwa sugar din yawa to sai ta mayar kan wuta bayan minti daya kacal sai ta sauke ta samu faranti mai fadi sai ta juye a ciki, shi ma sau ta yayyanka kamar yadda tayi a hadin farko shikenan ta kammala..
( *Banbancin su kawai shine hadin farko ba a daka gyadar gaba daya sannan ana zuba butter kafin a zuba sugar wanda wannan butter din tana karawa hadin kyau da santsi saboda gyadar da ba a daka sosai ba wannan butter zata taimaka wajen daidai ta laushin sa idan ana ci a baki*)
0 Comments