>> YANDA ZAKI KAWAR DA NANKARWA BAYAN HAHUWA <<
Sakamako huruwar fatan ciki lokacin renon ciki, bayan haihuwa fatan takan yamutse tayi zane-zane (Nankarwa) wanda yake tsufar da fatan wajen, saidai akwai hanya dazakibi domin dawoda fatan cikinki daidai kamar baki taɓa haihuwaba.
Ga wani Haɗi na shafawa kala biyu wanda zai taimaka sosai wajen kawarda Nankarwa.
>> ABU NAFARKO <<
KISAMU: Ɗanyen ƙwai guda 1 kifasa kicire ƙoduwar kibar sauran ruwan (Yolk) saiki markaɗa timatir babba guda 1 kizuba akan ruwan ƙwai ɗin sai kisa zuma chokali 2 da madarar ruwa saiki gauraya sosai.
Maimakon madara zaki iyasa ruwan lemon tsami.
Zaki dinga shafa wannan haɗin akan Nankarwar kibarshi yayi mintuna 30 ko awa ɗaya saiki wanke da ruwan ɗumi.
>> ABU NA BIYU <<
Bayan kin wanke sai kisamu waɗannan mayukan kihaɗasu duka kidinga shafawa:
1- Bitter Almond oil
2- Man Lalle
3- Man Kwakwa
4- Man Habbatussauda
5- Man Zaitun
Zaki dingayi safe da dare har zuwa lokacin da zai koma daidai yanda kikeso saboda da yanda jikinsa yake.
Haɗin farkon zaki iya haɗawa dayawa ki ajiyeshi a wuri mai sanyi saboda zai iya lalacewa.
0 Comments