ALAMOMIN BUƊAƊƊEN FARJI NA MATA WATO YADDA ZAKI GANE KO KINADA BUDADDEN GABA TARE DA YADDA ZAKU TSUKESHI
Yanayin halittar farji tamkar robar danƙo ce wacce zata iya buɗewa idan aka yi mata talala, haka kuma zata iya komawa ta haɗe, wato ta tsuke bayan buɗewa. Tsokokin bangon farji masu motsi ne kuma zasu iya tsukewa ko buɗewa idan mace tayi yunkurin tayi hakan, wato idan ta motsa su ko matse su ta ciki. Buɗaɗɗen farji (loose vagina) ko buɗewar farji (vaginal looseness) wani yanayi ne dake shafar mata da yawa musamman lokacin juna biyu da kuma bayan haihuwa inda farji ke canza yanayin halittarsa ya ƙara girma, wato ya zama buɗaɗɗen wuri kasancewar naman dake zagaye da farji mai yiwa zakari zobe lokacin jima'i ya saki , tsokokin sun saki basu iya damƙar zakari yanda ya kamata lokacin saduwa. Kamar dai yanayin halittar fatar jikin mutum, wasu mutanen fatarsu nada tauri kamar roba marar sauƙin budewa idan aka jata, wasu kuma fatarsu nada laushi da sauƙin yin talala idan aka jata, kusan haka itama halittar gaban mace take. Wurin haihuwa jinjiri na fitowa ne ta farji inda wurin ke buɗewa sosai domin jinjiri ya fito. Bayan wani lokaci da haihuwa farji na komawa ya tsuke . Duk da haka , farji ba zai taɓa komawa ba kamar yanda yake ada ko kamar na macen da bata taɓa haihuwa ba (ko budurwa) , koda kau anbi hanyoyin magani , farji zai zamanto ya ƙara girma kaɗan ko da yawa.
Yawan haihuwar mace, budewar gaba saboda tiyatar likita/ƙarin kofa a lokacin haihuwa (tear) da yawan yin jima'i yau da gobe, na daga cikin dalilan dake haddasa budewar gaban mace. Idan buɗewar farji tayi yawa yana zama kalubabale ga ma'aurata. Zaya iya zama matsala a rayuwarsu ta jima'i . Saboda wannan yanayi na sanya raguwar ɗanɗanon jima'i ga mace da mijinta koma ya hana macen jin ƙoluluwar daɗi (orgasm) lokacin saduwa. Dalilin faruwar haka shine , farji baya matse/riƙe zakari da kyau, ta yanda za'a samu ɗanɗanon gugar fata-da-fata tsakanin ma'aurata biyu wanda jin wannan guga shine zai kai ma'auratan biyu ga gamsuwa mai ƙarfi a lokacin jima'i. Bugu da ƙari, wannan matsala na iya saka mace cikin damuwa da jin cewa bata amsa sunanta na cikakkiyar mace ba saboda bata jin dadin saduwa kuma bata iya gamsar da mijinta da kyau. Hakan kuma zai iya sanya maigidan ya ƙara wani aure domin biyan buƙatarsa. Hakika gamsuwar aure itace saduwa mai daɗi tsakanin ma'aurata da zata samar da soyayya da zaman lafiya mai ɗaurewa. Matsatstsen gaba (tight vagina) bakin gwargwado, yanayi ne mai kyau da zai iya ƙarawa mace gishirin soyayya mai ƙarfi tsakaninta da mijinta.
YAYA ZA'AI KI GANE CEWA KO KINA DA BUƊAƊƊEN GABA?
1. Mafi yawan mata masu fama da matsalar buɗaɗɗen gaba na fama da matsalar rashin riƙe fitsari , wato ɗigar fitsari. Digar fitsarin zata iya faruwa a lokacinda kika ɗauki wani abu mai nauyi, ko lokacinda kika yi dariya, tari, ko atishawa. Wannan alamace cewa mace nada budadden gaba.Yawan shekaru, yawan haihuwa , yawan jima'i, tiyatar likita (ƙarin kofa) ko wani rauni a gaban mace, ko tsayawar al'ada (menopause) saboda karancin sinadarin "estrogen" na iya sanya raunin tsokokin farji wanda daga ƙarshe zai iya haddasa buɗewar tsokokin bangon farji masu matse zakari .
2. Hanya ta biyu da zaki iya sanin ko kina da gaba mai faɗi itace: ki saka ɗan yatsanki guda (manuni) cikin gabanki sa'annan kiyi ƙoƙarin matse dan yatsan da tsokokin farjinki. Idan har ki gwada yin hakan kuma ya zamanto baki iya jin kina matse dan yatsan da farji to zaya iya zama kina da babban wuri. Bugu da ƙari, idan kika saka yatsa 2 ko 3, misali manuninki da kuma yatsan tsakiyar hannnunki (mafi tsawo) , kuma baki ji wata alamar bangon farjinki yana matse yatsun ba to yiwuwar itace kina da buddden farji.
3. Idan ya zamanto yana da wuya kamin kiji ƙololuwar dadi (orgasm)/kawowa lokacin saduwa. Yana iya yiwuwa alamar budadden gaba ne. Haka kuma, raguwar jin dadi ba kamar daba shima na iya zama alamar.
4. Idan ya zamanto mace tana wasa da gabanta domin biyan buƙatarta kuma tafi sha'awar ta saka wani babban abu a gabanta akan ƙarami - wato bata jin dadin ƙaramin abu idan ta saka a farji sai babba. Shima alamace cewa mace nada girman farji. A baya munyi bayani da tsoratarwa akan wasa da gaba. Yana da illa ga lafiya da rayuwar auren 'ya mace. Don haka sai a kiyaye.
5. Idan ya zamanto kina shan wahala kamin ki gamsar da mai gidanki wajen jima'i ba kamar daba.
6. Idan ya zamanto sai kin matse ko haɗe cinyoyin ki biyu sosai sa'annan kike jin dadin jima'i da maigidanki. Wannan ma yana iya zama alamar budadden gaba. Duk da dai cewa wani lokacin yana iya zamantowa mijin ne keda ƙaramar al'aura. Amma idan kamin haihuwarki babu wannan matsalar sai daga baya to sai ki zargi budewar gaba.
7. Idan ya zamanto kina jin ƙarar fitar iska daga farjinki lokacin da maigidanki yake saduwa dake , iskan kamar fitar "tusa" amma ba tusa bace (fanny farting) kuma babu wari. Iskan yana shiga yana fitowa lokacinda maigida yake kaikawo. Wannan alamace kina da budadden farji.
MINENE HANYOYIN TSUKE FARJI ?........
Muhadu a karatu nagaba Insha'Allahu.
Kukasance Da Wannan Zaure Mai Albarka Don Sanin Makama Da maganin Matsalolinku dayardar Allah.
0 Comments