Ticker

6/recent/ticker-posts

Header Ads Widget

Responsive Advertisement

YADDA ZA'A MAGANCE WARIN HAMMATA DA GUMI A LOKACIN ZAFI


 YADDA ZA'A MAGANCE WARIN HAMMATA A LOKACIN ZAFI:


Akwai abubuwa da dama da ke haifar da warin hammata, musamman ma lokacin zafi. Yawan sanya kaya matsatsu ko kuma kaya sau biyu a lokacin zafi, duk sukan haifar da irin warin hammata. Idan mutum kuma ya kasance mai yawan shan giya, ba wuya zai yi warin hammata.


Don haka ne a yau na kawo muku hanyoyi da za a bi domin rabuwa da wannan matsala:


🍋A samu lemun tsami a raba biyu a goga a hammata bayan an yi wanka. Ko kuma a matse ruwan sannan a samu tawul a rika tsomawa, a rinka shafawa a hammata bayan an yi wanka kafin a sanya tufafi. A rika yin haka don magance wannan matsala.


🍓‘Rose water’ na taimakawa wajen magance warin hammata. Don haka sai a rika diga ruwan a cikin ruwan wanka, sannan a shafa a hammata bayan an yi wanka.


🍅A matse ruwan tumatiri sannan a shafa a hammata na tsawon mintuna 15 sannan a shiga wanka. Amma irin wannan zai dan dauki lokaci kamar mako daya kafin a rabu da warin hammata.


☕Amfani da alumu “alum “na taimakawa matuka. Sai a tsaoma alum a ruwa, sannan a shafa ruwan a hammata a bari ruwan ya bushe. Yin hakan na magance warin hammata.


🍶Hodar jarirai na magance warin hammata, domin tana dauke da kamshi sai a rinka shafawa a hammata a kullum bayan an fito daga wanka.



Post a Comment

0 Comments