Ticker

6/recent/ticker-posts

Header Ads Widget

Responsive Advertisement

ABUBUWAN DA SUKE SANYA MACE TA RIKA JIN ALAMUN JUNA BIYU AMMA IDAN TAYI AWO SAKAMAKON YA NUNA CEWA BABU CIKIN


ABUBUWAN DA SUKE SANYA MACE TA RIKA JIN ALAMUN JUNA BIYU AMMA IDAN TAYI AWO SAKAMAKON YA NUNA CEWA BABU CIKIN


👩🏻‍⚕️👩🏻‍⚕️👩🏻‍⚕️👩🏻‍⚕️👩🏻‍⚕️👩🏻‍⚕️👩🏻‍⚕️👩🏻‍⚕️👩🏻‍⚕️👩🏻‍⚕️👩🏻‍⚕️👩🏻‍⚕️👩🏻‍⚕️👩🏻‍⚕️👩🏻‍⚕️👩🏻‍⚕️👩🏻‍⚕️


Hakika mata da yawa suna korafi akan wannan matsalar a halinda da ake ciki yanzu. Abubuwa masu yawa suna iya haifar da wannan yanayin. Amma bisa nazarin da nayi, muhimman abubuwan da suke kawo shi sune:


1. Dalili na farko shine hasashen samun juna biyu wanda ake kira "phantom pregnancy" ko kuma "pseudocyesis". Shi yanayi ne wanda yake sanya mace ta rika ji ko ganin dukkan alamomin samuwar juna biyu, kamar rashin zuwan jinin al'ada a lokacin da ya saba zuwa mata (missed period), ko zazzabin safe (morning sickness), ko ciwon nono (breast tenderness), ko tashin zuciya (nausea), ko yawan gajiya (fatigue), ko motsi irin na jariri a ciki (fetal-like movement), da sauransu. Duk da wadannan alamomin, idan mace tayi awon ciki sakamakon zai nuna cewa babu cikin. Babban abinda yake haddasa shi shine tsananin kwadayi da zakuwar samun juna biyu. Ma'ana, idan mace ta kosa ta samu juna biyu, to, kosawar zata sanya jikinta ya fara zubo da sinadarai daban-daban irin wadanda suke zuba a jikin mai juna biyu, daga nan sai dukkan alamun juna biyun su tabbata a gareta.


2. Dalili na biyu shine idan halittun jikin mace masu alaka da haihuwa (reproductive organs) suka kamu da rashin lafiya, to, zata rika jin alamun juna biyu. Misali, idan tana da matsalolin mahaifa (uterine disorders), ko rashin daidaiton zubar ruwan sinadarai (hormonal imbalance), ko matsalolin nono (breast disorders), ko matsalolin jakunkunan ruwan sinadarai (hormonal gland disorders), da sauransu.


3. Dalili na uku shine juna biyun sinadarai (chemical pregnancy). Wannan yana faruwa ne idan mace tayi barin karamin ciki (early pregnancy miscarriage). To, maiyiwuwa ne ta rika jin alamun juna biyu bayan tayi barin, domin jikinta ya fara samar da ruwan sinadarin human chorionic gonadotropin (hCG).

4. Tasirin sinadarin zai ci gaba da haifar mata da alamun juna biyu bayan tayi barin, sai a hankali zai daina.


4. Dalili na hudu shine samuwar cikin bayan mahaifa (ectopic pregnancy). Idan kyankyasasshen kwan haihuwa ya makale a jikin bututun fallopian tube, maimakon a cikin mahaifa, to, mace zata rika jin alamun juna biyu, amma koda tayi awon ciki sakamakon zai nuna cewa babu cikin, saboda yawan sinadarin hCG da jikinta yake samarwa bashi da yawan da zai nuna cewa akwai cikin.


5. Dalili na biyar shine yawan amfani da magungunan gargajiya da na bature ba bisa ka'ida ba. Yin hakan zai rikirkita jikin mace, har ta rika jin alamun juna biyu alhalin kuma bata dashi, domin ko anyi awon ciki sakamakon zai nuna cewa babu.


A takaice, idan mace tana ji ko ganin alamun juna biyu amma awon ciki ya nuna babu, to, a binciki wadannan abubuwan da na lissafa a sama.


Wadannan kari ne akan abubuwan da 'yan-uwa suka fada na amfani da magungunan tazarar haihuwa, molar pregnancy, da sauransu.


Allah SwT ya kawo ciki da goyo mai amfani, amin.🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻


 Don't forget to share please.



Post a Comment

0 Comments