DALILAN DAKE KAWO KAIKAYIN GABA GA MATA DA KUMA MAGANIN WARAKA DAGA CUTAR HARDA MAGANCE INFECTION
Anan, za mu kalli wasu daga cikin abubuwan da suke haifar da kaikayin gaba ga mata.
● YEAST INFECTION.
Yeast Infections na daya daga cikin sanannun abubuwan da ke haifar da kaikayin gaba ga mata.
Wannan infections din suna faruwa ne sakamakon yawaitar wani nau'in fungus da ake kira Candida.
Canje-canjen hormones, yin amfani da antibiotics, da wasu magunguna na iya haifar da yeast Infections.
Mata masu juna biyu suma suna iya fuskantar kamuwa da yeast Infections, sakamakon samun chanje chanje na hormonal yayin daukar ciki.
Yeast Infections yana iya haifar da zafi da jin ƙaiƙayi.
Hakanan kuma yana iya haifar da jin zafi yayin jima'i ko lokacin fitsari, da kuma canje-canje a cikin ruwan dake fita a gabanki.
Ruwan da kike fitarwa na iya zuwa fari kamar koko kuma mai kauri kamar kindirmo kindirmo.
● BUSHEWAR GABA.
Bushewar gaba shima yana daya daga cikin sanannun abubuwan da ke iya haifar da ƙaiƙayin gaba.
Zaki iya fuskantar karancin ruwa a gabanki wanda hakan kan iya haifar da kaikayi.
Ana iya samun karacin ruwa ta hanyar canjin hormones, musamman ƙarancin estrogen.
Kina iya fuskantar wannan yanayi musamman bayan haihuwa ko yayin shayarwa.
Bushewar gaba ya fi zama ruwan dare a yayin da kike tunkarar shekarun daukewar al'ada (menopause), ko kuma kina daf da lokacin daukewar al'ada(perimenopause).
A lokacin da kike daf da lokacin daukewar al'ada, canjin hormones da karancin yawan oestrogen na iya haifar da bushewar gaba akai-akai da ƙaiƙayin gaba.
● BACTERIAL VAGINOSIS (BV)
Bacterial vaginosis (BV) wani Infection ne da ke faruwa sakamakon yawaitar ƙwayoyin cutar bacteria dake gaban mace. Manyan alamomin sa sune ƙaiƙayi, radadi, fitar ruwa mai launin toka, da wari mai kama da karnin kifi. Yana iya haifar da zafi lokacin da kike fitsari ko kuma jin ƙaiƙayi daga wajen gaban ki.
● CUTUTTUKAN INFECTIONS DA AKE SAMU TA HANYAR JIMA'I.
Cututtukan Infections da ake ɗauka ta hanyar jima'i (STIs) na iya haifar da ƙaiƙayin gaba, zafi, da rashin gamsuwa.
STIs suna iya samuwa ta dalilin cututtuka daban-daban, ciki har da chlamydia, herpes genital, trichomoniasis da gonorrhea.
Zafi da kaikayi na daga cikin alamomin wannan infection.
Sannan kuma yana iya zuwa da rashin jin daɗi yayin jima'i, jin zafi a lokacin fitsari, zafin ƙashin ƙugu, da fitar ruwa ba yadda aka saba ba.
● Bugu da kari, ga wasu daga cikin abubuwan da kan iya haifar da kaikayin gaba sune chemicals da ake samu acikin mayukan dake kashe kwayoyin maniyyi (contraceptive cream), omo, sabulu, turare ko kuma duka wani abu da zai iya kaiwa zuwa gabanki kai tsaye.
MAFITA GA MATAR DAKE FAMA DA KAIKAYIN GABA.
kafin muje zuwa ga magungunan da kan iya taimakawa wajen kawar da wannan kaikayi.
Muna sake sanawar akan online courses da muka shirya akan mutanen dake fama da matsaloli masu zuwa don samun mafita da izinin Allah:
■ Raunin jima'i da saurin inzali
■ Matsalolin istimna'i
■ Sabbin Angwaye.
Wasu daga cikin tsirrai da ke taimakawa wajen kawar da ƙaiƙayin gaba sune kamar haka:
■ Cinnamon (girfa): Cinnamon yana dauke da anti-fungal da anti-inflammatory properties, Sannan kuma ana yin amfani da ita ta hanyar hada garin girfa da ruwa a rika shafawa a wurin da abin ya shafa daga nan kuma a wanke da ruwan dumi.
■ Ganyen na'ana'a: Ana iya tafasa ganyen na’a a da ruwa sannan a barshi ya wuce sai a wanke wurin da abin ya shafa a hankali, saboda na'ana'a yana ɗauke da sinadarai masu sanyaya jiki da kuma hana kumburi.
■ Cucumber: Za a iya nika kokwamba kadan a gauraya shi tare da yoghurt, sannan a chakuda a shafa a wurin da abin ya shafa don samun saukin kaikayi da kumburi.
■ Tafarnuwa: Tafarnuwa anti-fungal ce ta dabi'a kuma tana taimakawa wajen hana ci gaban yaduwar candida a gaban mace. Kuna iya cin tafarnuwa aƙalla guda ɗaya a rana don kawar da kaikayin gaba.
■Baking Soda Bath:
Bincike ya nuna cewa sodium bicarbonate, wanda akafi sani da baking soda, na iya hana ci gaban funguses. Mutane da yawa sun bayar da rahoton cewa baking soda yana taimakawa a lokacin da suke da yeast, wanda ke faruwa sakamakon yaduwar fungus. Ɗaya daga cikin hanyoyin mafi sauki da za a yi amfani da baking soda don maganin yeast Infections shine baking soda bath.
An bada shawarar zuba kusan kofi hudu na baking soda a cikin don sakamako mafi kyau.
Daga karshe kula da tsaftar ki sosai a lokacin da kike fuskantar ƙaiƙayin, kuma hanya ce mai sauƙi, marar lahani don sarrafa ƙaiƙayin gaba. Wannan na iya haɗawa da wanke yankin farjinku da sabulu mara chemicals wanda aka hada da abubuwa na dabia ko kuma aki yin amfani da sabulun kwata-kwata (ruwa kawai). Yakamata ki kiyaye kar kibar gaban ki da danshi sannan ki saka wando wanda kaso 100% cotton ne.
ALLAH YA BAWA DUK WASU MARASA LAFIYA, LAFIYA.
0 Comments