Ticker

6/recent/ticker-posts

Header Ads Widget

Responsive Advertisement

DALILAN DAKE KAWOMA MACE CIKI BAYAN MAHAIFA WATO (ECTOPIC PREGNANCY) DA YADDA ZAKU KIYAYE FARUWAR HAKA DON KAUCEWA MATSALA


 DALILAN DAKE KAWOMA MACE CIKI BAYAN MAHAIFA WATO ECTOPIC PREGNANCY DA YADDA ZAKU KIYAYE FARUWAR HAKA DON KAUCEWA MATSALA YAKAMATA KOWACCE MACE TASANSU DON KIYAYE FARUWAR HAKAN 

  


        (AMSA)

_ECTOPIC PREGNANT: Shine bayyanar ciki acikin bututun mahaifa da kwayayyen halittar mace ke bi su shigo zuwa cikin mahaifa maimakon cikin ya kasance acikin mahaifa kamar sauran cikkuna.


Yakan faru bisa kididdiga a dukkan mace 1 daga cikin mata 50 masu ciki.


ABUBUWAN DA SUKE KAWOSA


)1- Shigar kwayoyin cuta zuwa cikin shi wannan bututun (Fallopian tubes) wanne sukansa bututun ya dod'e koma toshe baki daya.


2)- Idan antaba ma mace aiki (operation) a kugunta wanda hakan ya bar tabo a jikin bututun.


3)- ko kuma ya zamto tube din yasami kansa a yanayi na kara girma akaran kansa kamar yadda kwayoyin cancer kanyi.


Wadannan sune mahimman abubuwa uku dake kawo sa. 


TOU SAIDE AKWAI WASU ABUBUWA KAMAR ACE RISK FACTORS DAKE JAWOSA SUMA


1- Daga ciki akwai Pelvic Inflammatory Disease(PID)


2- Sai kuma anfi ganinsa a matan da suka kai shekara 35 zuwa 44.


3- Sai wacce in abaya ta ta6a samun matsalar zata iya kuma maimaitawa


4- Wacce ta rika zubda ciki abaya ta hanyar shan magani ko kuma ta hanyar cire mata shi.


5- kowacce ya zamto cikin irin dasa mata shi akai ta hanyar zuba maniyyin direct acikin mahaifar.


6- Wacce ta biyo ta hanyar shan magungunan samun haihuwa, wacce Kila da cikin yaki samuwa.


ALAMOMIN ECTOPIC PREGNCY


---Jin zafi kamar an yanki ko cakawa mutum wuka a ciki, mara, akafada ko a wuya, lokaci lokaci.


-- Fitar jini agaba alhalin ansan ba haila bace.


-- In ya zamana ga ciki Amma kuma ana ganin jinin haila na fita da yawa ko kuma kadan.


-- Yawan Jin yamutsewar ciki


--Yawan kasala


-- Ganin jiri.


TAYA AKE IYA GWAJI A GANOSA ?


▶- Likita na iya fahimtar sa ta hanyar duba marar mace dan fahimtar inda take jin zafin, Sannan zai daddana yaji ko akwai tauri, ko taushi sosai,ko alamar inda wani Abu ya taru a matakin farko.


▶- mataki na biyu Akansa ayi ultrasound domin agani ko cikin a mahaifar yake ko awaje.


▶- Akan auna level din hcG din mace dan agani shin yayi kasa (low) bisa yadda ake tsammanin sa ya kasance. Inyai kasa za'a iya suspecting din ectopic.


▶- Akan auna sinadarin halitta mace na progesterone (sex hormones) Shima agani ko yayi kasa.


▶- Sannan likita na iya amfani da wata hanya mai suna Culdocentesis wacce hanya ce da ake bi asa allura ta tsakanin saman farji sosai kasa da mahaifarta daga gaban hanyar da tai dubura ta baya domin ganin ko akwai jini awajen, samun taruwar jini awajen Shima na iya nuna alamun ectopic.


Allah Ya kara Muna lfy da zaman lafiya Amin.





Post a Comment

0 Comments