WAI KO KINSAN ABUBUWAN DAKE CIKIN WAYAR ‘YARKI KUWA A MATSAYINKI NA MAHAIFIYARTA KO KUMA MARIKIYA???
Barkanki da war haka. Kina da budurwa a gabanki? Tana da wayar hannu na zamani da take amfani da shi? Kin taba daukar wayan nata kin duba abubuwan da suke ciki? Idan baki taba ba, to ce mata ta miko maki wayar yanzu haka idan kina da lokacin dubawa.
Shiga akwatin ajeyan sako inbox na wayar ‘yar taki, kanwarki, ko mawacece da take gaban naki ki duba sakonnin cikinsa daya bayan daya. Kin duba inbox, to shiga ki duba sakonnin da ita kuma ta turawa wadanda suka aiko mata da sakonnin nasu wato send items, kin duba? Yanwa jeki whatsapp dinta nan ma bishi daya bayan daya ki duba, kin gama? To leka facebook dinta massinger da istargrame shima bisu ki duba irin hotunan datake posting. Hmmm kin gama dubawa?
Kin gama duba wadannan, to yanzu shiga ma’ajiyar hotunan da bidiyo na wayar wato Gallary, bisu ki dubasu guda bayan guda suma ba tare da kin tsallake ko guda cikin su ba kuma ki rika kula sarai da abubuwa da suke kunshe cikin wayar. Duba shafukan internet datake shiga.
Daga nan kuma ki koma jerin sunayen da suke cikin wayar nata daya bayan daya kina duba sunayen dake ckin wayar tare da neman bayanin ga dukkanin wani sunan da kika gani kuma bakiyi amanna da shi ba.
Kiku sanyawa ‘yar datake gabanki idanu a duk lokacin datake amsa wayar da aka bugo mata da kuma wayar data buga, tana kebewa domin kada kiji abunda take cewa ko kuma a gaban kowa take amsa wayar kowa?
Wadannan sune hakkin daya rataya akan kowace macen datasan da cewa da akwai ‘yan mata balagaggu a gabanta kuma wadanda suke amfani da wayar hannu na GSM da yanzu haka ya zama ruwan dare gama duniya a hannayen kwailaye, ‘yan mata, zaurawa matan aure har ma da kurame mata da ma bebaye.
Shi dai wayar sadarwa na salula, wayace data shigo a wannan zamani wacce kuma take da alfanu ga rayuwar al’uma da daman gaske, wanda alfanun nata yanada wuyar gaske a iya misaltasu saboda yadda alfanun nasa ya zama tamkar farilla a mallaketa.
Don haka ne yanzu haka wayar ta zama tamkar jumfa a Jos a hannu koda da kowa a wannan lokaci musamman ma ‘yan mata da kuma matasa wadanda wasu iyayensu ke sanya kudi masu dan karen tsada su sai musu wasu kuwa samarinsu ne ko kuma kawayensu ke basu ko sai musu.
Haka kuma iyaye da daman gaske musamman wadanda suke da farar zuciya game da ‘ya’yan nasu basu damuwa da neman sani ko irin wadannan wayoyin na ‘ya’yan nasu suna kunshi da wasu abubuwa wadanda suna iya gurbata tarbiyan ‘ya’yan nasu da kuma jefesu cikin halaka.
Wasu iyayen musamman na zamani kuwa da suke da masani akan irin wadannan abubuwa marasa kyau da ‘yan mata kan sanyasu ciki wayoyinsu na GSM, basu damu da su bincika ba bare kuma su takawa ‘ya’yan nasu birkin da zasu kawo karshen ganin cewa sun hanasu sanya irin wadannan abubuwa a cikin wayoyinsu.
Babu wanda zai iya misalta irin alfanun da wayar GSM yanzu haka take da shi a cikin al’uma, haka nan kuma babu mutumin daya isa ya kawo yawan barnar da GSM take haddasawa cikin wannan lokacin. Kamar yadda zaki iya samun biyan bukata da amfani da karamar waya mai arha, haka nan ma kina iya ajiye mugayen kalamai a cikin karamar waya mai arha.
‘Yan mata ne su uku muka hadu dasu a gidan buki, dukkanninsu kuwa basu wuce shekaru 16 zuwa 18 da haihuwa ba, ko waccensu tana da waya mai dan karen tsada a hannunta, wanda a kalla zasu kai naira dubu dari da ashiri zuwa talati na naira ko waccensu.
Guda daga cikin ‘yan matan ta sanni ta hanyar yarta, wanda hakan ya sanya ta gabatarwa sauran kawayen nata biyu da cewa nice Ummancy ta mujallar FIM, su kuma nan take suke shiga yimini tambayoyin maimakon ni namusu.
Muna cikin hira ne sai naga guda daga cikin ‘yan matan nan ta kunna wayarta inda naga wakar nan mai taken Abaje yana tashi kuma naga ‘yan tsanoni sunata bajewa, nan take na jawo hankalinta domin nuna mata cewa shekarunta sunyi kadan data rika kallon irin wadannan fina finan. Sanya bakin guda daga cikin kawayen nata ne ya canza tunanina akan ‘yan matan gaba daya.
Domin bayan da kawar ta sa baki tace “gaskiya Anti Umma yi mata fada donma baki shiga wayar nata bate sosai har bulu fim tana da shi a cikin wayanta”. Ita kuwa guda da jin haka sai tace “bulu fim bake da wacce (ta nuna ta ukunsu) kusa sanya mini ba”. Wannan yasa jikina yayi sanyi, sai kuma tunanin jaridanci ya fadomini maimakon yi musu wa’azi.
Nan take na sauya tsarin wa’azin nawa na soma da nuna musu cewa duk da yake da akwai hadarin mallakar irin wadannan hotunan bidiyo a wayoyinsu, suna iya yin kaffa-kaffa da shi domin kada wani da suke jin kunya su gani. Su kuma nan take dukkanninsu uku suka ammsa mini da cewa ai wayoyinsu da makullin da ba kowa zai shiga ba batare da sun bude masa ba.
Ganin yadda suka saki jiki dani bayan dana sausauto ne na nemi na duba wayoyin nasu daya bayan daya da sunan nima zan kofi hotunan batsa da kuma hotunan bidiyon dake cikin waoyin nasu ne, a wannan lokacin ne nasha matukar mamakin akan abubuwan dana gani a cikin wayoyin wadannan ‘yan matan da idan mace ta gansu zata rantsai da wanda ya halliccita wadannan yaran basu san yadda namiji da mace suke kwanciya ba.
Na fara ne da wayar kanwar kawata, mai karatu zakiyi mamaki idan nace miki naga hotuna a cikin wayan nan sun fi 500, haka kuma naga hotunan bidiyo wanda sun haura 50 kala kala. Kama da daga ‘yan mata masu manyan nonuwa da manyan duwaiwuka, sai kuma bidiyo da hotunan mata masu wasa da gaban maza, ga kuma mata da mata suna wasa da junansu. Hakan kuma yake cikin wayoyin sauran ‘yan matan biyu dana duba.
Bayan na kammala yiwa wayoyin nasu kallon kwakwaf ne dai, sai kuma na koma da tambayansu daya bayan daya ko mai yasa suka ajiye wadannan hotunan a wayoyinsu?
“Ni dai haka kawai nake ajiyesu a wayata, domin idan ina kwance ni kadai na rika kallon a bina. Wani lokacin kuma idan muna makaranta ne muke kallo” guda daga cikinsu tace.
“Ni dai a gaskiya saurayina ne yake sanya mini a cikin wayata duk lokacin daya zo hira wajena, idan yanada wani sabo wanda bani dashi sai ya turamini, ni kuma idan mun haduda kawayenmu wadanda suke da sabbi su bani nasu nima na basu nawa da basu da shi” ta biyu kenen take fada.
“Ni dai na kusa aure ne shi yasa nake sakawa na wayata ta rika kallo ina koyo kamin lokacin aurena yayi, amma kuma a gaskiya ina ganin sanya irin wadannan a wayoyin ‘yan mata marasa aure irinmu yanada matukar hadari, domin a gaskiya Anti naga kawayenmu da daman gaske da suka halaka ta hakan nima ina ganin dana koma gida yau zan goge dukkannin fina finai da kuma hotunan banza dake ciki” shawarar data ukunsu ta yanke kenen.
Bamu rabu da wadannan ‘yan matan ba saidana tabbatar da cewa nayi masu wankin kwakwaluwar dasuka goge wadannan hotunan da kuma bidiyon nan take, tare kuma da nuna masu hadarin dake kunshe da adana irin wadannan a cikin wayoyinsu kamar yadda wata daga cikinsu ta soma nunawa.
Don haka idan ke kanki uwace ko kuma wacce wata ‘ya budurwa ke gabanta ne a yanzu haka, to ki dauka cewa wadannan ‘yan matan dana zanta dasu a gabanki suke, kuma nan take bayan karanta wannan shafin ki maida hankali wajen kula tare da sanya idanuwa akan naki ‘yan matan.
Sai dai kuma, kada iyaye suyin tunanin cewa zasu raba ‘ya’yansu da wayoyin dake hannunwansu saboda Ummancy tace ‘yan mata na sanya hotunan batsa a ciki, abun yi a yanzu shine ki dai tabbatar da cewa akai akai kina duba abubuwan dake kunshe cikin wayar ‘yar taki, haka kuma ki tabbatar da cewa dukkanin lambarwar dake cikin GSM dinta kinsan kona wanene, ki kula domin wani lokacin suna da bagararwa ta hanyar sanya wasu inkiyoyi a cikin wayoyinsu a sunayen da basuson a sansu.
Domin naga ‘yan mata da damar gaske da iyayeynsu suka hanasu rike waya, amma sai su sayi wayar su baiwa kawayensu ajiya a gidajensu, basu amfani da wayar sai bayan sun fita gidajen nasu. Wasu kuwa boye wayoyin sukeyi a cikin dakunansu idan su kadai ne, sai dare ya tsala su rika hira da abokan hiran nasu.
Haka kuma kada ki sake kiyi tunanin cewa zaki canza mata waya da karami wanda baya iya daukar hotuna, domin shima bazai zama shine zai kawo karshen matsala ba. Domin wasu dalibai mata manyan wayoyin suna taimaka masu wajen bincike ta shiga yanar gizo.
Ina ganin cewa, tunda dai yanzu haka wayar GSM ta zama wata irin annobar da bazamu iya rabuwa da ita ba, kuma bazamu iya raba ‘ya’yan mu da AI ba saboda alfanun da Suke dashi a wani bangare na rayuwa, babban abunda yafi wajen iyaye musamman mata shine sanya idanuwa ga ‘ya’yan mu da kuma daura ‘ya’yan namu akan turba na koyarwar na addini, ta haka ne kawai ‘ya’yanmu zasu iya kyamatar saka ko kallon duk wani abunda suke da masani akan haramcinsa a wajen MahaliccinMu, amma ba muzurai ko dukansu ko kuma hanasu amfani da waya ba.
Hakan kuma ba yana nufin su kuma 'ya'ya maza abarsu su babu bincike ba, suma ana sanya musu ido dai dai gwargwado.
Da fatan Allah Ya shirya mana zuri'armu baki daya.
0 Comments