Ticker

6/recent/ticker-posts

Header Ads Widget

Responsive Advertisement

WASU MUHIMMAN DABI'U 7 DA ZASU IYA LALATA FARJIN MACE IDAN BATA KIYAYE WADANNAN ABUBUWAN BA


 WASU MUHIMMAN DABI'U 7 DA ZASU IYA LALATA FARJIN MACE IDAN BATA KIYAYE WADANNAN ABUBUWAN BA



Da akwai wasu halaye da dabi'u da mata da dama suke aikatawa wadanda suna iya cutarda gabansu sannu a hankali basu sani ba.


Akasarin mata da suke aikata wadannan dabi'un ko dai suna sane suke aikatawasu, ko kuwa akwai jahiltar illar abunda suke yi.


Gasu zan lissafo:-


1: Wanke Farji Da Kowani Irin Sabulu- Mata da dama suna amfani da duk wani sabulun wankan da suka samu domin tsaftace gabansu. A maimakon haka suke illata kansu saboda rashin sanin irin sinadarin dake kunshe cikin wadannan sabulan da mata ke wanke gabansu da dasu.

Akasarin sabulan dake canza launin fata suna dauke ne da sanadarin da suke yiwa gaban mace illa. Don haka sai ku kiyaye.


2: Zama Da Jikanku Kaya- Musamman Matan da suke shiga rafi wanka ko tafkin wanka na zamani. Ko kuma ruwan sama ya daki mace har tayi tsamo-tsamo a jike.

A irin wannan yanayin muddin mace na zama wani lokaci da jikankun kayan a jikinta wannan yana haifara da warin gaba kuma yana iya sa mace illa idan bata kula saboda cututtuka na bacteria da zai iya shiganta ta farkayan 


2: Kwanciyar Barci Da Matsantsu Wanduna-  Wasu matan suna kwanciya ne  da kayan dake matsaisu sosai,  Wanda yakan hana iska ratsa farjinsu. Wannan ba dai-dai bane. Rashin samun giftawar iska a farjin mace na iya baiwa kananan cututtuka daman shiganta. Shi yasa likitoci da dama suke bada shawaran mata su daina kwanciya da kaya a jikinsu ko kuma su rika saka Wanduna da zasu sha iska. Bafa ina nufin ki kunnawa gabanki fanka ba tom


3: Yawan shan madaran yogurt ga mata- babban illa ne amma mata dama sun daukeshi abun shansu. A cikin sinadaren da ake hada madarar da ita an gano wasu masu dauke da sinadaren dake ciki da kai tsaye suke yiwa farjin mata illa. Idan mace tana yawan sha yana iya sa gabanta wari.

Madara da cin kayan itatuwa sunfi amfani a jikin mace mace maimakon yogurt.


4: Shan Taba, Wiwi Ko Shisha-  Wadannan nan shaye shayen kai tsaye suke lalata farjin mace saboda hayakin dake shiganta.

Shi hayaki kai tsaye yake shiga jikin mutum kuma ya zauna. Shi yasa duk mai shaye shaye irin na hayaki kana ganinsa zaka gane. Musamman taba sigari yana dauke ne da abunda take jawo warin gaban mace.


5: Rashin Chanza Audugar Al'ada Akan Lokaci- Yana da kyau mace ta rika canza gunzugun al'adanta daga lokaci zuwa lokaci domin gudun kamuwa da cuta.

Akalla duk bayan awanni uku zuwa hudu mace ta canza kunzugunta.


6: Kula Wajen Wanke Farji-  Wasu matan idan sun tashi tsaftace gabansu suna cusa sabulu har can ciki wanda hakan yana yiwa gaban mace illa sosai.waje wajen gabanki wajen lungunan dake saman farji sune abun kula wajen tsaftacewa da sabulu.




Post a Comment

0 Comments