Ticker

6/recent/ticker-posts

Header Ads Widget

Responsive Advertisement

YADDA AKEYIN HADIN KARIN TSAWON GASHI NA MATA KIZAMA AUNTY YALASH KUMA GASHINKI YAYI BAKI DA SHEKI


 YADDA AKEYIN HADIN KARIN TSAWON GASHI NA MATA KIZAMA AUNTY YALASH KUMA GASHINKI YAYI BAKI DA SHEKI.



Akwai hanyoyi da dama da mata za su bi domin samar da gashin kai mai tsawo.


            Abune mai sauki.

 Mata da dama suna son ganin kansu da gashi mai tsayi kamar na Indiya.


 Gashi na daya daga cikin ababen da ke dada wa mace kyau don haka, ya kamata mu kula da gashinmu sosai. Wannan hadin da zan rubuto muku na dada wa gashi maiko , wato yana hana gashi karyewa da sanya shi tsayi da laushi.


 Ina son a san cewa wannan hadin akan yi shi ne kamar sau biyu a wata. Idan mutum ya kasance mai yin wani hadi ne daban wanda ba wannan ba, ba ya kamata ana hada wannan salon gyaran gashi da wani daban in ba haka ba, sai a ga kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba.


Abubuwan da za'a bukata


Man Amla

Zuma

Ruwan dumi

Hadi


A zuba cokalin amla biyu a roba.

Sannan sai a zuba rabin cokalin zuma a cikin amla.


A sanya cokalin ruwan dumi kamar 2-3.

A juya hadin har sai sun cakudu da juna.

A taje gashi kafin a shafa wannan hadin a fatar kai.

A jira na tsawon minti 30.

A wanke kai da man wanke gashi (shampoo).


Amfani da man kwakwa; man kwakwa na sanya gashi laushi da tsayi da kuma santsi. Yana da kyau a rika shafa shi a gashin kai duk lokacin da za a yi kitso ko kuma a rika gauraya shi a cikin man kitso.


Man zaitun; wannan man na da mahimmanci sosai a jiki baki daya. Sannan kuma yana sanya gashi santsi da baki. Yana kuma rage furfura a gashi da kuma sanya gashi tsayi da baki da sheki da kuma kyau.


YADDA ZAKI HADA MAN TAFARNUWA DON GYARAN GASHI.


1- A yayyanka tafarnuwar, sannan a zuba a cikin tukunya mai dauke da ruwa mai zafi.


2- Azuba man zaitun cokali biyu akan tafarnuwa da ruwa. 


3- A daura hadin a kan wuta har sai ya dafu.


Sannan a jujjuya shi bayan an arage adadin wutar kadan sannan aci gaba da juyashi akai akai.


4- Ki bar wannann hadin da ya gabata a cikin tukunyar har sai ya yi sanyi, sannan a sanya shi a cikin rufaffen mazubi har sai zuwa lokacin da za'ayi amfani da shi akan gashi.


ALLAH YA BAWA DUK WASU MARASA LAFIYA, LAFIYA.



Post a Comment

0 Comments