Ticker

6/recent/ticker-posts

Header Ads Widget

Responsive Advertisement

ABUBUWAN DA SUKE KARAWA MACE NI'IMA DA DANDANO WANDA ZAKI SARRAFA SU DA KANKI AGIDA


 ABUBUWAN DA SUKE KARAWA MACE NI'IMA DA DANDANO WANDA ZAKI SARRAFA SU DA KANKI AGIDA


ku sani cewa wadannan abubuwan da zan lissafo suna da matukar muhimmanci da amfani ga jikin mace hade da samun karin ni’imar sune kamar haka:-


1. *Tuffa (Apple)* matsayinta a jikin ki zai kara miki ni’ima a jiki har kasauki kuma jikinki ya ringa laushi yana kyau ba kamar wasu matan ba inka taba jikinsu ka ji tauri.


2. *Ruwan abarba:*

Shi ma yana da kyau mace ta rinka markadawa tana tacewa tana sha da sugar ko zuma.


3. *Rake:* 

Shi ma yana karawa mace ni’ima kuma yanada amfani matuka a jiki, yanda yake da zakinan da ruwa to haka mace zata ringa jin ni’imarta na karuwa.


4. *Aya:*

Shi ma duk tafiyar su daya da rake, ayar anaso irin bula-bulanan tana da matukar muhimmanci gurin mace tana da ni’ima kubar rainata hakama kunun aya idan yaji madarar peak.


5. *Zaitun:*

man zaitun yana magunguna da yawa to anaso ki ringa shafashi ajikinki yana gyara fata dasaka sautsi jiki, hakama yanada kyauki dinga shafawa a gabanku, yana saka laushi hakama idan mai gida yana iya shafawa.


6. *Bawon Bagaruwa:*

Shi kuma wani sirri ne wanda idan mace na son ta zama kullum a tsuke kamar sabuwa ta dunga dafa bawon ta na shiga kamar yanda ake shiga ruwan dumi in kin haihu.


7. *Tsumi:*

akwai tsimi mai kyau da mara kyau mara kyau yana tsinka jikin mace wata har jini yake sata na ba gaira ba dalili. Ga hadin tsumi ki yi da hannun ki yafi kyau ki nemi sasaken baure, kananfari, zuma, citta, mazarkwaila. Za ki tafasa sasaken baure ya dahu sosai sai ki daka kanumfari me yawa da citta yar kadan ki zuba akai, ki saka mazarkwailan da zuma amma zaki cire icen kafin ki zuba hadin, sai ki sauke ki dinga sha daidai kima idan ya huce.


8. *Ku samu zogale ku wanke shi ku nika shi tare da dabino da kuma kwakwa sai ku tace kusa zuma tare da madara sai ku saka ya yi sanyi bayan kungama sallar magrib sai ku sha.*


*Bayani kan wanda basajin dadin saduwa*

Ana so mace ta kula da gabanta domin Allah ya sa namiji ya kwallafa ransa gare shi. Barinsa ya lalace kamar zubar da kimarki ne a wajen sa kada ki bar shi ya yi wari, kada ki bar shi ya yi fadi. Domin masana sun ce duk lokacin da aka yi jima’i farjin mace yana karafadi shi kuma nasa yana rage girma to kinga nasa na rage girma na ki na fadi zai kuma ba kya kula da shi, ba zai rika jin gamsuwa ba. Don haka sai ya fara tunanin kin tsufa ke ma ki fara ganin ya za ma rago shi ya sa yawanci ba a samun gamsuwa. 


Kuma ba kowane namiji ba ne zai iya fadawa matarsa gabanta ya kara girma ba. Don haka mu kula.


*Macen da takeso gabanta yayi cif cif* sai ta samu farar albasa, kanunfari, citta, balmo, barkono, rihatul hulbi. Sai ki hada su waje daya ki mayar da su kamar yaji kina zubawa cikin abinci kina ci kullum.


*Mijinki ma za ki iya masa hadi,* ki sami muruci, saiwar haukufa, namijin goro, hanno, rihatul hubbi ki daka su gaba daya, ya dinga zubawa a nono mai kyau sha. Sannan ku nemi dabino a daka shi ya sa a cikin nono mai tsami sai ya rika kama ruwa da shi, amma fa bayan ya gama shafawa zai iya wanke wa da ruwa.

Insha Allah za a samu biyan bukata. Allah ya taimake mu amin.


    *""Karin Bayani""*

Cuta daga Allah ne kuma ya aiko mana da maganin kafin ya sauko da cutar. Don haka mu san ba abin da ya fi karfin magani. *Shawara ita ce* a yawaita shan zam-zam, insha Allahu magani ne ba adadi. 


Allah ya ba mu lafiya baki dayan mu!



Post a Comment

0 Comments