WASU HANYOYIN DA ZAKI TSAFTACE GABANKI DA KUMA YADDA ZAKI KULADA KANKI LOKACIN AL'ADA WATO (PERIOD)
Maza ma'aurata sukan fahimci tsaftar matan da suke aure ta hanyar yadda suke kula da gabansu.
Akwai matan da zaka gansu a wajen tsaf kamar wanke hannu ka taba, da za kayi arba da kazantar da suka tattara a farjinsu abun zai bada mamaki. Hakan kuwa na faruwa ne saboda rashin iya tsaftace al'auran su.
Ga wasu hanyoyin da zaki iya kula da tsaftar gabanki domin inganta rayuwar aurenki.
1: A Lokacinda kika zo tsarki musamman bayan kinyi bayan gida.
Ki tabbatar da cewa kin wanke duburanki sosai domin a wani lokacin wajen rashin wanke wajen yadda ya kamata ana samun feshin ruwan wanke duburan dake da burbudin kashi yake fesowa gaban mace ganin yadda duburan mace da farjinta suke da makotaka.
Wannan yasa wajen yin tsarki koma bana bahaya bane mace ta tsafta ce duburanta sosai.
2: Yin fitsari duk bayan kammala Jima'i shima hanya ne na tsaftace gabanki.
Kamar yadda mukayi bayani a wasu darusa a baya. Yanada kyau mace ta sha ruwa kamin ta soma Jima'i domin samun damar yin fitsari bayan kammala Jima'i.
Ana samun wasu cutuka dake shiga gaban mace a yayin jima'i. Haka nan maniyi na iya makalewa a tsakanin farjinta da mafitsaranta.
Yadda ta hanyar yin fitsari ne kawai wadannan abubuwan zasu iya fita daga gaban mace amma ba wanke gabanta ba.
Wannan yasa wasu matan sai gabansu yayi ta wari duk kuwa da kokarin da suke yi na tsaftace shi. Don haka yin fitsari bayan duk wani jima'i ga mace zai taimaka mata wajen tsaftace gabanta.
3: Kada kice zaki wanke gabanki da sabulun dake sauya launin fata. Irin wadannan sabulen wari kawai suke jawowa gaban mace saboda irin sinadarin dake kunshe dasu.
Kyauta ki samu sabulun da bai da wannan sinadaren domin tsaftace gabanki dashi.
4: Kiyi kokarin yawaita sauya kamfenki musamman idan yayi gumi ko kuma ya jima a jikinki.
5: Haka nan ki zamanto mai tsaftace gabanki da yawan sauya auduganki a lokacin al'adar ki.
Muddin mace zata kiyaye wadannan abubuwan babu shakka gabanta zai kasance cikin tsafta da ban sha'awa ga mazan dake son yin wasa da gaban matansu.
YADDA ZAKI KULA DA KANKI LOKACIN HAIDHA WATO (PERIOD)
'Yar uwata ki riqe azhkar na safe da yamma matuqar riqewa yayin da kika cikin al'ada
Ki kula da kanki jikinki tufafinki da muhallinki matuqar kulawa ki ninka tsaftarki fiye da baya
Mafi qarancin wanka kiyi sau biyu a rana_ki canza pad a duk awa shida,da amfani da turaruka masu qamshi,kuma nisanci amfani da ruwan sanyi
Idan da hali ki ware pant daban da zakina amfani da shi na iya lokacin ne kawai,idan kin gama ki wankesu da gishiri ki shanya a rana ki goge ki ajiye sai kuma next time
Idan kina ciwon Mara kije asibiti a dubaki a baki maganin data dace dake ,ba kowanne magani zakina sha ba
Ana samun sauyawar halayayya a wannan lokacin wasu saurin fushi wasu yawan kuka wata kasala,yawan fada gashinan dai abubuwa da yawa,kiyi qoqarin sanar da wadanda suke kusa dake,kamar miji mahaifiya saboda a fahimceki
Ki san irin abubuwan da zakici a wannan lokaci ki nisanci abubuwan zaki ko miyar yauqi ko yawan fita bada dailili ba
Kiyi amfani da lokacin wurin karatun sauran littafan addini da azhkar da sauran ibadunki na musamman
In zaki fita daga gida kiyi shirinki mai kyau da tufafin da suka dace da yanayin, kiyi guzurin pad a jaka saboda bakisan inda yanayi zai riske ki ba
Kisan adadin kwanakinki da yanayin zubar jinin idan kikaga sauyi ki tuntubi masana da likita da wuri
Sanin ilmin haidha wajibi ne a kanki ki bada himma sosai wurin fahimtarsa da hukunce hukuncensa har zuwa daukewarsa,ki iya banbance komi
Bayan haidha ki tsaftace kanki sosai kiyi amfani da ganyen magarya da miski da cin abinci mai kyau,da sauran abinda ya kamata.
Bayan kin samu tsarki ki sake sabon tsarin karatunki da ibadunki na nafila fiye da watan baya
Allah ya muku Albarka ya sa mu dace.
0 Comments