YADDA AKE GYARAN FATA DA LALLE GA MATA DA IRIN SIRRIKAN DAKE TATTARE DASHI LALLEN TARE DA YADDA ZAKI MAGANCE INFECTION DA LALLEN.
Lalle dai da farko wani sinadari ne mai dauke da alfanu iri iri, kuma addini ya kwadaitar da mata su yi lalle akwai sirrika acikin sa bafa Lallen bature nake magana ba Lallen Hausa.
Nafarko dai lalle Kariya ce daga sihiri, Kariya ce daga aljanu sannan kuma Kariya ce daga cututtuka da dama, yin lalle a kafa na zuqe cutar dake kafan sannan yana kula da dumin mace, bi ma ana yana kiyaye. ni imar mace ba tare da ya gushe ba, innace lalle wasu zasu dauka zanen henna nake nufi ko, to lalle dai na gargajiya wanda muka rabu da yinsa yanzu shi nake magana akai:
Ga kuma sadaqa ga duk mai infection ta tafasa lalle inyadan huce sai ki dinga zama a ciki na sati biyu, in Allah yayarda za ki warke.
: Saboda maganin da lalle keyi ma akan iya shan ruwan lalle cokali daya don wankin dattin ciki amma banda masu ciki, to yanzu dai zamu dauki bangare daya daga cikin amfanin lalle muyi magana akai, wato shine amfanin lalle da kuma yanda ake amfani da shi don gyaran Fata.
Lalle dai ba karamin tasiri yake dashi wajen gyara fata ba, domin shi natural toner ne ba bleaching yake ba amma yanasa haske mai kyau kuma yana goge dattin fata, in kina son gyara fuska tai kyalli, laushi da haske to ki kwaba lalle da ruwan Kwai amma banda kwaiduwar kwan ki kwaba ruwa ruwa amma ba sosai ba ki lizimci shafa shi kullum minti talatin kafin wanka, za ki sha mamaki in sha Allah:
Ga masu son hasken fata, ki kwaba lalle da ruwa, ki shafe a jikinki inya bushe ki dirje da man zaitun zakiga canji.
sannan gamai son kamshin fata
: Ki kwaba lalle da turaren ki mai kyau na ruwa wanda ake durawa ki zuba isasshen ruwa a bucket ki sa garin lalle ya jika yay já zir sai ki tsiyaye ruwan ki diga turaren ki mai kamshi ciki Bayan kinyi wankan sabulun ki sai ki dauraye jikinki dashi inkin lizimci haka to bake ba rabo da kamshin jiki in sha Allahu.
: Sannan ga gyaran duka jiki kuma zaki hada lalle da sabulun salo da Zuma kina wanka dasu duk zakiga canjin fata in sha Allah
Sannan ga Amare kuma
Kafin kiyi dilke na aurenki zaki iya fara gwada na Lallen Nan.
0 Comments