Ticker

6/recent/ticker-posts

Header Ads Widget

Responsive Advertisement

KALAMAN DA DUK WATA MACE TAKE MATUKAR SON JINSU DAGA BAKIN MIJINTA A LOKACIN JIMA'I

KALAMAN DA DUK WATA MACE TAKE MATUKAR SON JINSU DAGA BAKIN MIJINTA A LOKACIN JIMA'I


Maza da dama dauka suke mace ce kadai ake bukatanta da yin sumbatu a yayin gudanar da kwanciyar aure.

Kaman yadda duk wani namiji bai son yaji matarsa tayi gum kamar kurma idan ana saduwa da ita, haka suma mata basa son jin mazansu sunyi tsit a lokacin Jima'i dasu.


Ga wasu kalmomin da suke tunzura mace idan namiji na furta matasu a yayin saduwa da ita.


1: Zan Jiyar Dake Dadi: furtawa matarka wannan kalmar na bata tabbacin cewa zaka gamsar da ita a Jima'in ku na wannan lokacin.

Wannan furucin yana karawa mace karfin gwaiwa gami da kara shiga shaukin kamuwa da mijinta.


2: Tsaftarki Na Daban Ne: Mace tana son jin mijinta ya yaba da tsaftar jikinta da kuma kamshi ko taushi na jikinta.

Kalmomi irinsu, "duk inda na daura hancina a jikinki kamshi kawai ke tashi. Ina yabawa da tsaftarki. Jikinki tamkar auduga". Kalamai ne da suke kara sa mace ta sake ta kuma kara sakin jiki da mijinta.


 3: Ganin Tsairaicinki Kawai Na Gamsar Dani: mata da dama suna kunya ko tsoron gwabewa a gaban mazansu ne saboda gudun kushe yanayin jikinsu.

Akwai mata masu banyan cibiya misali. Wata duk jikinta narkanwa. Wata kuwa tabo ne a jikinta. Wata gwamece, wata kuwa tumbi ne ya mata yawa. Wannan yasa wasu matan duk da ba a haka suka zo gidan mazajensu ba, amma sai su rika kunyar tsairaici.

Wannan kalmar na son ganinta a kwabe kalmace da zai bata karfin gwaiwar da zata saki jiki ta bayyana maka tsiraicinta ba tare da wani fargaba ba.


4: Yawun Bakinki Shine Ke Bani Dandano: wannan furucin na tabbatarwa matarka cewa kana bukatar jin bakinta a naka ma'ana sumbatar juna. Sumbatar ma irin na musayan yawun baki.

Wannan zai sa nan take ta kamo harshenka da bakinka da tsotso.


5: A Kullum Kina Gamsar Dani: Bata tabbacin yadda take kwantar ma da hankali da gamsar dakai a Jima'ince.


Tabbatar mata babu wani abunda ta gaza a fannin gamsar da kai.

6: Babu Macen Da Zata Fahimceni Irinki: Kwarzan tata ta hanyar tabbatar mata da cewa, ba duk mace bace zata iya lakantarka kamarta.

Sanar da ita a duk duniya itace macen data fahimceka a Jima'ince.


7: Kina Dauke Mini Hankali Akan Wasu Matan: Mace zata so sanin yadda take gamsar da kai nasa ka manta cewa akwai wasu matan banda ita.

Nuna mata gaba daya hankalinka da soyayyar ka duk yana gareta.


8:Ko A Aljanna Babu Sauyi: Yi mata albishir na cewa bama anan duniya ba, ko a Aljanna tare zakuci gaba da rayuwa a matsayin miji da matarsa.


9: A Kullum Kara Dadi Kike: Ka tabbatar mata tana kara shekaru, tana kara dadi.

Nuna mata a kullum gansuwar da take baka yafi na baya. Nuna mata yanzu ne ma kafi jin dadinta fiye da lokutan baya.


10: Sumbatu Ki Sani Saurin Inzali: Nuna mata kana matukar son yadda take maka sumbatu, kukan kissa da kukan raki.

Fahintar da ita, muryar datake amfani da shi idan kuna Jima'i yafi duk wani abun busawa dadin sauraro.


11: Ni'imar Ki Samar Da Nawa: Sanar da ita wannan ni'imar da kake kwasa daga gareta na danshin gabanta suke tabbatar maka da dacen da kayi na auren mace irinta.


12: Takace Ita: Tabbatar mata babu mai rabaku bare har wani ya samu wannan baiwar da kake samu daga gareta.


Nuna mata irin kishin da kake dashi akanta saboda yadda ta lakanceka, yadda take gamsar da kai.


Wadannan Kalaman zuga da kambawa ga matarka idan kuna Jima'i, kalamaine da duk wata mace zata wuni tana tilawarsu saboda tasirinsu.


Kalamai ne da suke karawa mace son mijinta. Kalaman sukansa mace a kullum taji tanada bukatar mijinta. 

Wadannan kalaman suke bambamta mutum da dabba a lokacin saduwa. Shi dabba yana nasa kalaman ne domin a bashi. Shi kuma mutum yana yinsu ne kamin a bashi, bayan an bashi da kuma bayan ya gama. 


Da fatan maza ba zasu rika saduwa da matansu da baki a rufe ba kamar Wani kurma ko kamar wanda aka bashi tutu yaciba.




Post a Comment

0 Comments