YADDA AKEYIN HADIN HADADDEN ALKUBUS NA ZAMANI ME LAUSHI GA DADIN GASKE
KAYAN HADI:-
Alkama
Fulawa
Yeast
Gishiri
Mai
Sugar
YADDA AKE SARRAFAWA
1. Da farko za a tankade garin alkama da na fulawa a hade su waje guda, sai a zuba yeast da sugar da gishiri a kwaba, amma yafi na fanke tauri.
2. A rufe a kai shi rana, idan ya tashi sai a zuba mai kadan a kara buga shi.
3. Sai a dauko gwamgwani a na shafa masa mai ana zubawa a ciki, ko kuma kukkula a leda kamar Alala.
4. Sai a turara shi. Ana ci da miyoyi irin daban daban
NOTE:- za,a iyayin na na flour zallah kona Alkama zallah kuma za,aiya hada biyun ayisu.
Duk miyan dakuka gadama zaku amfani dashi ko Miyar Egushi ko Stew ko source.
0 Comments