Ticker

6/recent/ticker-posts

Header Ads Widget

Responsive Advertisement

KUSKUREN DA SUKE BATA DANDANON GIRKI WANDA YAKAMATA UWARGIDA DA AMARYA SU KIYAYESU WAJEN GIRKI


KUSKUREN DA SUKE BATA DANDANO A GIRKI WANDA YAKAMATA UWARGIDA DA AMARYA SU KIYAYESU WAJEN GIRKI


✔idan kinsan girkinki ke kadai ce kobeda yawa kiguji yawan amfani da gishiri domin kuwa muddin kina saka wadataccen maggi to gishiri zedinga miki yawa


✔duk abinda kikasan zaki barshi ya kwana kiguji saka mishi kwai kokuma madara musamman idan ba fridge zakisa ba


✔kilura gurin sarrafa kifi beson jagwalgwale hannu yana saurin bata kifi kidinga kulawa


✔kilura idan kanwarki bata da kyau kobaki da isasshe kokuma baki da ita tokarkiyi danwake domin kuwa bazae taba yin dandanoba hakanan kada kice zaki yawaita shi


✔sphagetti batason spices dayawa hakanan bata son adafa ta da tafassahen nama ko ruwan nama dandanonta beyin dadi sedae kisoya nama kijefa aciki kokuma kisaka mata kifi hakanan koda wasa karkisakawa sphagetti kitse


✔kilula idan zaki soya chips gishiri kawae ya wadatar karkice zaki saka maggi hakan ba gata bane taste din bekai na gishirin dadi


✔gurin yin waina wato masa kikula sosai albasa tana kara dadi amma idan tayiwa waina yawa tana bata taste din karkice zaki kwaba ta da albasa koki markada yana sakawa albasar tajima tana bugan kullin har taste din ya chanja


✔ba ayin farfesu babu daudawa kikula koda na kifi ne daudawa itace sirrin farfesu hakanan cikawa farfesu Mai ko manja nasa taste din yakoma wani abu daban


✔kikula wajen dafa black tea bakowanne irin ganyayyaki ake sakawa ba anfison ganyen yazmato kala guda sauran kuma kayan kamshine idan bahaka ba zeyi daci ko bauri


✔kikula gurin yin peper meat ko chicken dole sekin dan soya sannan kisake hadeshi idan bahaka ba zeyi karni


✔ita tafarnuwa anfison asoyata ne afarkon girki nanne taste din yake dadi amma karkice zaki zubata akarshen girki zaki gagara ci musamman miyar kadi hakanan ba asaka tafarnuwa a alale ko dambu da makamantansu

anan zandakata bawae don sun kareva se zuwa next term insha Allah zamuci gaba dasauran girke girken zamani domin yau mun tabo bangaren girkin yau da kullum ne.



Post a Comment

0 Comments