Ticker

6/recent/ticker-posts

Header Ads Widget

Responsive Advertisement

YADDA AKEYIN AWARA KALOLI DABAN-DABAN MASU KYAU DA DADI NA ZAMANI


YADDA AKEYIN AWARA KALOLI DABAN-DABAN MASU KYAU DA DADI NA ZAMANI


INGREDIENTS 

Waken suya

Kwai

Attaruhu

Albasa

Mai 

Maggie 

Gishiri

Ruwan tsami ko Dan Tsami

Manja kadan

 

         YADDA ZAKIYI SHINE

Da farko zaki gyara waken suya se ki wanke ki rege ki kai inji a markado idan aka kawo se kisa manja kadan saboda yana hana kullin lalacewa daga nan se ki tace da Abin tata seki dora idan kin dora a wuta idan yakusa tafasowa saiki tsaya kusa kada yayi kumfa yazuba daya tafaso Saiki zuba Ruwan tsaminki ko jikakken tsami da jajjagaggen kayan miyanki zakiga yafara hade jikinsa yadunkule idan yanuna yagama hade jikinsa zaki ga ya dunkule idan yayi saiki samu buhu mekyau ko Abin tata saiki kwashe aciki.


Ki kulle kulle duka yakullu sosai kidora abu menauyi akai ruwan yagama fita.

Idan yagama tsanewa saiki kwanceshi kan faranti ki yayyanka dai-dai yadda kikeso sai soya abinki da kwai idan kuma da source zakuci koda yaji ko miya duk yadda kikeso haka zakuyi awara ta kammala muhadu a Wani girkin nagaba inshAllah



Post a Comment

0 Comments