Ticker

6/recent/ticker-posts

Header Ads Widget

Responsive Advertisement

YADDA AKEYIN HADADDEN BANDASHE WATO GURASA ME DADI UWARGIDA AMARYA AZO AKOYI GURASA DON RAMADAN AYIMA OGA

YADDA AKEYIN HADADDEN BANDASHE WATO GURASA ME DADI UWARGIDA AMARYA AZO AKOYI GURASA DON RAMADAN AYIMA OGA:


KAYAN HADIN GURASA:

man gyada,

dakakken kuli,

tumatiri,

gurji,

koren tattasai,

albasa,

yajin barkono,

sinadarin dandano.


             YADDA AKE HADAWA:

Da farko uwargida za ta tanadi kulinta dakakke, ko ita ta daka ko kuma ta sayi dakakken. A qulin ana sa sinadarin dandano, wasu ma harda kayan kamshi. Daga nan sai a samu ‘yar roba a zuba ruwa. Idan uwargida na son dandano ya fito sosai, sai ta dan zuba gishiri a ruwan, ko kuma in gurasan mai sukari ce ana dan zuba gishiri a ruwan.

Daga nan sai uwargida ta tanadi abinda za ta yi amfani da shi wajen turara gurasarta. Wasu matan da madambaci su ke yi wadda ake yi musamman domin turara abinci. Wasu kuma suna da madambaci namu na gargajiya, wasu ma da mataci suke amfani. Akwai wàdanda suke kulle gurasar a leda su jefata cikin tukunya mai tafasar ruwa.

Idan uwargida ta daura madambacinta a wuta, sai ta dauko gurasa guda daya ta dan sata a ruwan na roba da ta tanada, yadda za ta dan jike, domin kuli ya zauna sosai a jikinta. Idan gurasan ta debo ruwa sosai uwargida na iya matseta. So ake tayi danshi ba jiqewa ba.


 Ana sa gurasan a kwanon kulin a juyata gaba da baya. Daga nan sai sa gurasar cikin abin turarawar, haka uwargida zatayima ragowan gurasan.

In an gama ko kuma in madambacin ya cika, sai a rufe don su turaru. Yayin da gurasa ke turaruwa, dama uwargida ta yanka tumatiri, albasa, koren tattasai, da gurji, sannan ta soya man gyada da albasa.

Bayan mintina kadan uwargida ta duba gurasar, Idan tayi laushi sannan ta fara qamshi, to ta turaru. Da anfito da gurasa daga wuta se a zuba mai a kanta gaba da baya, a kawo wannan kayan lambu a zuba, se kuma yaji daidai yadda uwargida ke buqata. Za a iya kara kuli inda buqata. 


Wasu sukan yanka gurasan qanana, ko kuma a barta yadda take in anzo ci a yanka da wuka ko cokali mai yatsu. Wasu ma da hannunsu kawae suke ci.




Post a Comment

0 Comments