Ticker

6/recent/ticker-posts

Header Ads Widget

Responsive Advertisement

YADDA ZAKI GANE FITAR FARIN RUWA MAI ILLA DA WANDA BEDA ILLA DA KUMA ABUBUWAN DA SUKE IYA KAWOSHI

 

YADDA ZAKI GANE FITAR FARIN RUWA MAI ILLA DA WANDA BEDA ILLA DA KUMA ABUBUWAN DA SUKE IYA KAWOSHI.



Kamar yadda na fada a baya Cewar mace na iya fitar da farin ruwa a gabanta throughout menstrual cycle dinta .Kuma wannan ba matsala bane ga lafiyarta 


Amma abubuwan da Suke kawo fitar farin ruwa a gaban mace Wanda ba na lafiya bane (abnormal) sun hadar da 


● STIs (Sexually transmitted infections ) kamar su gonorrhea,chylamydia,trichomonas duk (duk bacterial infection ne ) duk suna jawo mace ta ga farin ruwa a gabanta.

Gonorrhea da chylamydia, su yawanci basa ma nuna symptoms. Sannan discharge Dinsa yana yin  yellowish haka.


●Trichomonas discharge din da yake jawowa yana yellow Ko Kore ne haka ,sannan yana nuna alama kamar qarnin Kifi kuma ga kaikayi sossai. 


● Candidiasis (yeast infection) shi kuma discharge dinsa fari ne mai kauri kamar farin madara yawanci yana  da alama kamar kaikayi da jin zafi zafi a gaba


● BACTERIAL VAGINOSIS:- Shi kuma wata infection ne da yake jawo discharge (fitar farin ruwa a gaba ) mai kama da toka toka (grey white) sannan yana sa warin gaba kamar qarnin Kifi Kifi haka .


SHAWARA 

Idan mace taga farin ruwa yana fita a gabanta koma ya launin kalarsa yake  sai yake zuwa da wasu alamu na matsala yayin fitarasa kamar zafi , kaikayi,wari,kumburi,kuraje,dadewar fatar gaba, ta ciki ko waje,to maza maza aje aga likita domin a gano asalin abin da ya kawo matsalar bacteria ne ko fungi,ko parasite kafin shan magani kai tsaye. 



Post a Comment

0 Comments