Ticker

6/recent/ticker-posts

Header Ads Widget

Responsive Advertisement

GARGADI DA KULAWA DA KUMA IRIN TARBIYYAN DA ZAKIWA 'YARKI TUN TANA KARAMA KINUNA MATA DON TAKIYAYESU


GARGADI DA KULAWA DA KUMA IRIN TARBIYYAN DA ZAKIWA 'YARKI TUN TANA KARAMA KINUNA MATA DON TAKIYAYESU A MATSAYINTA NA MACE KEMA UWA SAIKI ZAUNA LAFIYA


 1.) Ki gargadi 'yar ki kada ta kuskura ta

zauna a cinyar wani, koda kanin babanta ne

ko Almajirin gidansu.

.

2.) Kada ki dinga canja kaya a gaban

'ya'yanki wadanda suka kai kamar shekara

biyu. Ki dinga cewa su fita.

.

3.) Kada ki yarda wani babban mutum ya

dinga kiran 'yar ki da "Mata ta" ko

"Amarya ta" dds.

.

4.) Idan 'ya'yanki suna wasa da wasu yaran,

ki dinga lura wane irin wasa sukeyi. Saboda

wasu yaran suna wasa da al'aurar junansu.

.

5.) Kada ki matsawa 'yar ki zuwa wajen

wanda ba ta so ta je wajensa. Kamar

wani me siyar da kayayyaki ko

makamancinsu.

.

6.) Ki saka lura sosai idan kika ga dan ki ko

'yar ki sun shaqu da wani mutum a waje

kuma suna son zuwa wajensa.

.

7.) Kada ki bari dan ki ko 'yarki su dinga

yawo ba riga ko wando a cikin gida balle su

fita waje.

.

8.) Idan kin yiwa 'yar ki kwalliya, to ki gaya

mata iya gidajen da za ta shiga.

Kuma daga nan ta dawo gida. Kada ta zauna

a rariya ko shige-shigen gidaje.

.

9.) Idan ki ka ji an yiwa abokin dan ki ko

kawar 'yarki wani abu mara dadi, to kema ki

binciki na ki sosai. Ki tuhume shi.

.

10.) Idan 'ya'yanki mata sun fara girma, ki

koya musu yadda ake kula da jini. Da yadda

ake kula da budurci da hadarin kawar da

shi. In ba haka ba zata fara koyar munanan

dabi'u a wajen kawaye.

.

11.) Ki kula da irin kayan wasan da yaranki

suke amfani da su. Kamar yartsana me

hoton tsiraici da makamantansu.

.

12.) Ki koyawa 'yar ki me shekara uku yadda

ake wanke muhimman gurare ajiki, har da

kirji kuma ki gaya mata kada ta bari kowa ya

ta6a mata nan wajen da nan wajen.

.

13.) Ki tabbatar duk wani hoto ko abin

amfani wanda zai 6ata tarbiyyar yaro kin

nisanta shi da inda yaranki za su gani.

.

14.) Duk sanda 'yarki ko danki ya kawo miki

karar wani babba ya cire masa

kaza ko ya ta6a masa kaza, to kada ki dau

mastalar da wasa.

.

A bi duk matakan da suka dace don

tabbatar da

abinda ya faru.

.

15.) Ku tuna Tarbiyyah tana farawa ne daga

gida


Pls kutura zuwa wani group din don sauran iyaye mata su ankarar da iyalansu



Post a Comment

0 Comments